Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban ?asa Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da abin da ya kira ‘kisan rashin hankali” da wasu ‘yan sanda da ke bakin aiki suka yi wa wata lauya mai suna Omobolanle Raheem ranar Kirsimeti.
A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ?asar Malam Garba Shehu ya fitar, shugaba Buhari ya ce ya yi matu?ar ka?uwa da jin labarin kashe lauyar,.
Sannan kuma shugaban ya umarci hukumomin ‘yan sanda da su ?auki tsattsauran mataki kan wa?anda suka aikata wannan ta’asa.
A wata mai kama da wannan ita ma hukumar kula da aikin ‘yan sanda ta Najeriya ta yi Allah wadai da kisan lauyar.
A cikin wata sanarwa da ta fitar mai ?auke sa hannun shugaban sashen hul?a da jama’a na hukumar Ikechukwu Ani, hukumar ta ce tana bu?atar rahoto kan kisan daga hukumar ‘yan sandan, da kuma kiran bayar da horo ga ‘yan sanda kan yadda za a ri?e makamai.
Tuni dai shugaban rundunar ‘yan sanda ta ?asa Usman Al?ali Baba ya bada umarnin kamowa gami da gurfanar da jami’in ?an sandan da ake zargi da yin kisan domin fuskantar hukunci.
Marigayiyar ta rasa ranta ne a ranar Kirsimeti akan hanyar su ta dawowa daga Coci tare da mijinta lokacin da ?an sandan ya yi harbin da ya kai ga rasa ranta.
