Kusan shekara ?aya bayan hawa mulkin Shugaba Bola Tinubu, Gwamnatin Tarayya ta kafa kwamitin mutum 28 domin su shirya shagulgulan cikar mulkin Tinubu shekara ?aya.
Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume ne ya kafa kwamitin, kuma ya rantsar da su a ofishin sa, a ranar Juma’a, kuma ya bayyana masu cewa dalilin hakan shi ne domin a bayyana wa ‘yan Najeriya irin ci gaban da wannan gwamnati ta samar cikin shekara guda.
Akwai Kwamitin Addu’o’i a Coci, Kwamitin Addu’o’i a Masallaci, Kwamitin ‘Yan Kai-kawo, Kwamitin Ka?e-ka?e da Raye-raye, Kwamitin Kula da Lafiya, Kwamitin Tsaro, Kwamitin Jaridu da Ya?a Labarai, Kwamitin Shirya Fareti, Kwamitin Shirya Lacca, Kwamitin Saukar Manyan Ba?i da Kwamitin Sakateriya.
Akwai mambobi irin su Femi Gbajabiamila, Shugabar Mai’aikatan Gwamnatin Tarayya, Folasade Yemi-Esan, Ministan FCT Nyesom Wike, Ministan Harkokin Ku?a?e, Wale Edun, Ministan Ya?a Labarai Mohammed Idris, Ministan Tsaro Badaru Abubakar, Ministan Gona Abubakar Kyari, Ministan Albarkatun ?asa da Ma’adinai, Dele Alake, Ministan Makamashi Adebayo Adelabu, Ministan Ayyuka, Dave Umahi, Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo.
Sauran sun ha?a da Ministan Lafiya Umar Fate, Ministan Harkokin Mata, Uju Kennedy-Ohanenye, Hadiza Bala-Usman da sauran su.
