ECOWAS Ta Umarci Dakarunta Su Daura Damarar Kai Yaki Nijar

Shugabannin ?asashen Ecowas sun ba da umarni ga dakarun sojin ?ungiyar, su ?aura ?amarar kai ya?i Nijar, bayan juyin mulkin sojoji na ranar 26 ga watan Yuli.

Sanarwar da Omar Aliu Toure, shugaban hukumar Ecowas, ya karanta bayan taron sirri da suka gudanar ranar Alhamis, shugabannin ?ungiyar sun ba da umarnin shirya dakarun ko-ta-kwana na Ecowas da yiwuwar tilasta wa Nijar aiki da ?udurorin ?ungiyar.

Sun cimma wannan matsaya ce yayin wani taron gaggawa da suka gudanar a Abuja.

Cikin sau?i, ba za a iya fayyacewa ?arara ba, ko umarnin yana nufin dakarun sojin Ecowas za su auka wa Nijar ne da ya?i, ko kuma za su ?aura ?amara su zauna cikin shiri kawai.

Tun da farko, Ecowas ta bai sojojin da suka yi juyin mulki wa’adin kwana bakwai, su mayar da Shugaba Bazoum Mohamed da suka ham?arar kan karagar mulki, ko su fuskanci amfani da ?arfin soja.

Shugabannin sun ce sun yi nazari kan rahotannin jakadun da suka aika, kuma sun yi muhawara cikin tsanaki a kan shawarwarin da manyan hafsoshin tsaron Ecowas suka bayar, da kuma sauran bayanan da hukumar ?ungiyar ?asashen ta gabatar.

Sun kuma nanata yin Allah-wadai da juyin mulkin Nijar da kuma ci gaba da tsare Shugaba Bazoum Mohamed.

?ungiyar ta ce za ta tabbatar da ganin ana aiki da duk ?udurorinta kuma har yanzu duk ?ofofi a bu?e suke. Shugabannin sun kuma ?ora wa jagororin Ecowas alhakin ci gaba da bin diddigin takunkuman da aka ?a?aba wa shugabannin juyin mulki a Nijar.

Haka zalika, sun garga?i wa?anda suka ce suna kawo cikas ga ?o?arin tabbatar da zaman lafiya a Nijar, su guji yin haka.

Related posts

Leave a Comment