ECOWAS Na Bukatar Sama Da Dala Biliyan 2.6 Wajen Samar Da Rundunar Tsaro – Ministan Tsaro

Ministocin Tsaro da na Ku?i na ?asashen ECOWAS sun yi ganawar a Abuja, babban birnin Nijeriya, inda suka tattauna kan yanke shawarar yawan dakarun da ake bu?ata da kuma yawan ku?a?en da ake bu?ata don samar da rundunar tsaron yanki.

Ministan Tsaron Nijeriya ya kara da cewa ba za a yi amfani da rundunar yankin wajen ?aukar mataki a kan juyin mulkin ba, illa kawai ya?i da ta’addanci.

?ungiyar Raya Tattalin Arzikin ?asashen Afirka ta Yamma ECOWAS tana bu?atar dala biliyan 2.6 duk shekara don samar da ?a??arfar rundunar tsaro da za ta yi ya?i da ta’addanci, a cewar ?aya daga cikin za?uka biyun da hukumomin tsaro na ?asashen yankin ke duba yiwuwarsu a taron da suka yi a yau Alhamis.

Ministocin Tsaro da na Ku?i na ?asashen ECOWAS sun yi taron a Abuja, babban birnin Nijeriya, inda suka tattauna kan yanke shawarar yawan dakarun da kuma yawan ku?a?en da ake bu?ata don samar da ita.

Afirka ta Yamma na fama da matsalolin juyin mulki, lamarin da yake zama matsala ga tsarin siyasa da jawo rarrabuwar kai tsakanin ?asashen yankin.

A watan Janairu, shugabannin mulkin soji na Nijar da Burkina Faso da Mali sun yanke shawarar ficewa daga ?ungiyar mai mambobin ?asashe 15.

Ministan Tsaron Nijeriya ya shaida wa taron cewa akwai za?i biyu a samar da rundunar yankin: Daya za a kashe dala biliyan 2.6 duk shekara a kan runduna mai dakaru 5,000, dayan kuma za a kashe dala miliyan 481 a dakaru 1,500

“Wadannan alkaluma sun nuna muhimmancin aikin da ke gabanmu,” in ji Badaru. “Don haka ya zama wajibi mu yi nazari sosai kan zabin duba da irin kalubalen da yankinmu ke fuskanta a halin yanzu da kuma matsalolin kudi da kasashe mambobinmu ke fuskanta.”

Tun a shekarar 2020, sojoji a kasashen uku suka yi juyin mulki suna zargin shugabannin farar hula da ?yale masu da’awar jihadi su samu galaba.

Da hawansu kan mulki, sojojin sun yi watsi da yarjejeniyoyin tsaro da aka ?ulla da sojojin Amurka da Faransa da kuma na Majalisar Dinkin Duniya tare da gayyatar Rasha da su maye gurbinsu.

Ministan Tsaron Nijeriya ya kara da cewa ba za a yi amfani da rundunar yankin wajen ?aukar mataki a kan juyin mulkin ba, illa kawai ya?i da ta’addanci. Ana sa ran kowace ?asa mamba za ta ba da gudunmawar wani kaso, in ji shi.

Shugaban hukumar ECOWAS Omar Touray ya ce ba za a cire mambobin da aka dakatar daga cikin rundunar yankin ba.

“An yi imanin ba za mu iya yaki da ta’addanci mu kadai idan har wasu ba su shiga ba,” in ji Touray.

“Ko da yake ana iya dakatar da wasu kasashe amma ya kamata a bar su su shiga tarukan da suka shafi tsaro, shi ya sa muka gayyaci dukkan kasashe mambobi 15 da su halarci wannan muhimmin taro.”

Related posts

Leave a Comment