Ministan ma’aikatar samar da hasken wutar lantarki a Najeriya, Bayo Adelabu ya ce yana cike da damuwa kan yadda ?angaren samar da wuta ke ci gaba da ta?ar?arewa a fa?in ?asar.
Ministan na lantarki ya bayyana haka ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, inda ya nuna ?acin ransa kan raguwar wutar lantarki da ake samu duk da irin kokari da ake yi a ?angaren.
“Dangane da haka ne na gayyaci shugabannin kamfanin rarraba wutar lantarki na Abuja (AEDC) da kamfanin rarraba wutar lantarki na Ibadan (IBEDC), da kuma Babban Darektan Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki ta Najeriya (TCN), zuwa wani muhimmin taro,” in ji ministan.
Ya ce makasudin kiran taron shi ne tattaunawa kan ta?ar?arewar wutar lantarki a yankunansu da kuma ganin an samar da mafita mai ?orewa kan hakan.
Mista Adelabu ya ce ma’aikatarsa ta yi ta matsa wa masu samar da wutar lantarki da su ?ara kokari a ayyukansu, abin da ya sa ma har aka ?ara karfin megawat na wuta zuwa 4000.
Ya ce duk da irin ci gaba da aka samu, wasu kamfanonin rarraba wutar lantarkin sun kasa rarraba wutar lantarki da TCN ke bayarwa yadda ya kamata, yayin da ake ?ara samun masu satar da kayayyakin wutar lantarki musamman a yankuna kamar Abuja, Benin, Fatakwal, da kuma Ibadan.
Ya ce ba za su lamunci rashin samar da wuta ba daga kamfanonin da alhakin haka ya rataya a wuyansu, kuma za a ?auki mataki mai tsanani a kansu, ciki har da soke lasisi.
Ministan ya ce ana ci gaba da tsare-tsare na ganin an warware basussukan da ake bin kamfanonin samar da wutar lantarki da iskar gas, wanda hakan zai rage wahalhalun da ake fama da su.
Don haka, ya bu?aci jama’a da su ?ara hakuri yayin da ake aiki tukuru wajen magance wa?annan matsaloli da kuma samarwa ?an Najeriya wutar lantarki yadda ya kamata.
