Dr Gumi Ya Yi Rabon Littatafan Addini A Rugagen Fulani

Rahotanni daga Jihar Kwara na bayyana cewar Babban Malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, ya kai ziyarar wa’azi Ilori, babbar birnin jihar Kwara domin ganawa da al’ummar Fulani da kuma gina gidauniya ta musamman.

Malam Gumi dai ya shahara da shiga cikin daji don ganawa da Fulani inda yake musu wa’azi kuma ya gina musu makarantu da rijiyar burtsatsai.

Bisa jawabin da Hadiminsa Salisu Hassan Webmaster ya saki a shafin Facebook, wannan karo, Malamin ya tafi garin Ilesha domin rabawa al’ummar Fulanin littatafan addini.

Malamin zai gana da Al’ummar Musulmai Fulani mazauna wani kauye tare da yi musu nasiha da kuma raba musu littafan addini da daura ginshikin gina musu mu’assah ta Sheikh Usman bn Fodio Foundation.

Cikin tawagarsa akwai Sheikh Sunusi Kutama, Sheikh Muhammad Adam Sulaiman, Farfesa Usman Yusuf da Mal. Murtala Abdullahi”

Sheikh Dr. Ahmad Abubakar Gumi ya yi Alla-wadai da yadda yan siyasa sukayi tururuwa zuwa daurin auren ‘dan Buhari da Zahra Bayero. Babban Malamin ya yi Alla-wadai kan yadda yan siyasa suka yi amfani da dukiyar al’umma wajen baja koli da hayar jiragen alfarma.

Malamin ya yi bayyana dalilin da yasa Malamai ba sa iya fadawa shugabanni gaskiya. Yace duk yan siyasa sun lalata Malaman addini shiyasa basu iya musu wa’azi, su fada musu gaskiya.

Related posts

Leave a Comment