Dole A Dakatar Da Kisan ‘Yan Arewa – Matawalle

“Ya zama dole a matsayina na gwamna kuma mai kishin Arewa da nayi magana akan abubuwan dasu ke faruwa a kasar nan. Wannan ba magana ce ta siyasa ba. Lokaci yayi da zamu fa?awa kanmu gaskiya domin dawwamar zaman lafiya da cigaban ?asarmu, da kuma kare Nijeriya daga afwaka tashin hankalin da wasu ?ata-gari ke son jefa ta a ciki.

Duba da yadda mukeyin siyasa a ?asar nan, za ayi tsammanin jawabi irin wannan daga gwamna ko wani shugaba na jam’iyar APC zai fito, ba ni ba cikakken ?an jam’iyar adawa ta PDP. Na yanke shawarar yin wannan jawabi ne saboda kishin Najeriya tare da neman wanzar da zaman lafiya da cigaban Arewa.

Abubuwa da dama, marasa da?i, na faruwa ga Arewa da kuma mutanen Arewa. A kullum ana kashe ?an Arewa, ana lalata dukiyoyinsu a wasu sassa na Kudancin ?asar nan duk da ?o?arin da shugabannin Arewa keyi na kwantar da hankalin mutanensu, da kare mutunci da rayuka, da dukiyoyin d ‘yan Kudancin Najeriya mazauna Arewa.

Duk da irin mawuyacin halin da ‘yan Arewa suka samu kansu musamman a Kudu maso Yamma da Kudu maso Gabas, shumagabanni da manyan mutane ?an Arewa sunyi shiru. Maimakon su marawa yankinsu da jama’arsu baya sunyi tsit, sa?anin mutanen Kudu wanda ke kare mutanensu koda kuwa basu da gaskiya.

Shiru da shuwagabanin Arewa sukayi duk da tsangwamar mutanensu da akeyi domin tabbatar da zaman lafiya a ?asa ba tsoro bane. Ko wace alumma zata iya dukkan abin da yakamata domin kare kanta in hakan ya zama dole. In dai ba za a tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin ‘yan Arewa a Kudancin Najeriya ba, to kada ayi tsammanin Arewa zata kare ‘yan Kudu mazauna Arewa.

A kwanakin baya an kashe ‘yan Arewa, aka ?ona dukiyoyinsu a kasuwar Sasa. Anyi hasara mai ?umbin yawa, amma shuwagabannin Yarabawa basu yi komai ba a kai, sai ma kare miyagun da sukayi wannan ta’asa da sukayi. Wasun su ma cewa sukayi lefin mutanen Arewa ne.

Biyo bayan kisan da aka yiwa ‘yan Arewa a jihar Imo ranar Lahadin data gabata, ya zama dole ayi Allah-wadai da kisan gilla da ?iyayyar da ake nunawa ‘yan Arewa a Kudancin ?asar nan. Ba zamu ?ara yadda a kashe mana mutane ba. Ko wane ?an Najeriya yana da damar yin kasuwanci a ko ina.

‘Yan Kudu na da tarin dukiya a Arewa fiye da ‘yan Arewa kedashi a Kudanci ?asae nan, amma babu wanda yake musu barazana. A koyaushe muna ?o?arin wanzar da zaman lafiya. In akayi duba na tsanaki akan rahotannin farmakin da ake kaiwa ‘yan Arewa a Kudancin Najeriya, za a gane masu son zaman lafiya, da wa?anda burunsu tada hankali to tunzura mutanensu.

Kowa ya san suwaye ‘yan iskan da suke kai farmaki (kan ‘yan Arewa), da wa?anda ke ?aukar nauyinsu. Mun san masu ya?a ?iyayya, da masu tada tarzoma. Amma abun takaici sun hana gwamnatin Tarayya ?aukar wani mataki akan haka; gwamnati ta zuba musu ido suna cin karensu babu babbaka. Najeriya ?asa ?aya ce. Duk wanda baya son cigaba da zamanta a dun?ule, yana da damar ?alubalantar tsarin mulki na ?asar, ko kuma ya tattara ya bar ?asar, amma ba ya ri?a yiwa was ?an ?asa barazana ba.

A matsayina na gwamnan jam’iyar PDP, ban yadda da siyasa ta ko-a-mutu-ko-ai-rai ba. Neman mu?ami ba zaya hanamu fa?in gaskiya ba, ko goyon bayan mutanenmu yayin da ake takalarsu da fa?a.

A matsayina na ?an Arewa, ina Allah wadai da yadda wasu suke cin mutuncin shugaba Buhari kuma suna nuna ?iyayya a fili ga Arewacin Najeriya da sunan zanga-zanga. Duk irin ?orafin dasuke dashi, ba hujja bane abinda sukayi. Abinda sukayi tsagoron jahilci ne, kuma ?atanci ne ga Shugaban ?asa. Wannan na tabbatar da irin ?iyayyar da ake nunawa Arewa. Zagin Shugaban ?asa ba shi ne hanyar isar da ?orafi ba. Zagin Shugaban ?asa ?as?anci ne da nuna ?iyayya, kuma shiri ne na Kudancin Najeriya, domin kuwa munsan wanda sukayi zagin da masu ?aukar nauyinsu. Doka ta amince da zanga-zanga ta lumana, amma amfani da zanga-zanga don cin mutuncin Shugaban Qasa, iyalinsa ko iyayensa (kamar yadda ya faru a Landan) abin takaici ne, abin Allah-wadarai ne. Da Buhari ?an Kudu ne, tabbas bazu yi masa haka ba. Maqasudin yin zanga-zangar shine muzanta Shugaban ?asa. Wannan yasa idan aka duba za a ga cewa masu zanga-zangar ‘yan tsirari ne, in akayi la’akari da yawan ‘yan Najeriya mazauna birnin Landan

Idan Arewa na son cigabanta, ya zama dole ta kare kanta, kuma dole shugabanni su jajirce wajen kare Arewa kamar, ko fiye ma da yadda ‘yan Kudu su keyi, a duk lokacin da aka ta?a musu mutum ko wani abu. Kada mu ji kunyar kare mutuncinmu kamar yadda abokan zamanmu keyi. Amma kada mu kare laifukan mu (kamar yadda suke yi). Najeriya ?asar mu ce gaba ?aya. Dole kowane ?an Najeriya yayi ?o?arin dauwamar da zaman lafiya. Dole a kare mutanenmu a Kudu a jiki, kamar yadda mu ke jan mutanen Kudu a nan Arewa. Muna fata tare da jankalin mutanenmu da su zauna lafiiya domin zaman lafiyar su a wajen shi zai

Sa hannu:
Alhaji Dr. Bello Mohammed,
(Matawallen Maradun),
Mai girma Gwamnan Jihar Zamfara

Related posts

Leave a Comment