Dattawan Yarbawa Sun ?alubalanci Gwamnati Kan Igboho

Labarin dake shigo mana daga Ikko babban birnin Jihar Legas na bayyana cewa Sakatare janar na kungiyar dattawan Yarabawa, Kunle Olajide ya bukaci antoni janar na kasa, Abubakar Malami ya zayyana wa ‘yan Najeriya laifukan da Sunday Adeyemo, mai rajin kafa kasar yarbawa, wanda aka fi sani da Sunday Igboho, ya aikata.

A cewarsa, hakan ne zai ba ‘yan Najeriya damar gane abinda gwamnatin tarayya take bukata a shari’ar da take shirin yi da Igboho.

Yayin da ya amince da cewa za a iya samun mafita a siyasance, Olajide ya ce ta yuwu shawarar da Malami yake ganin zata iya bullewa ta bambanta da ta wurin Buhari.

A ranar Talata, Malami ya ce gwamnatin tarayya zata iya gurfanar da dan tawayen bayan hukumar jamhuriyar Benin ta sake shi domin fuskantar hukunci.

A martanin da yayi dangane da furucin Malami, Olajide ya sanar da cewar zai zama shari’a biyu kenan idan har gwamnati ta gurfanar da Igboho bayan shari’ar da ya yi a kasar waje. Olajide ya ce ya kamata a yi dubi akan yadda jami’an tsaro suka halaka wasu mutan gidan Igboho Olajide ya ce a yi dubi da yadda jami’an tsaron gwamnatin tarayya suka afka gidan Igboho wanda har aka halaka wasu daga cikin mazauna gidan, ya bar Najeriya amma duk da haka rayuwarsa tana cikin hadari.

“Zai zama shari’a har biyu kenan. Wacce doka Igboho ya karya? Ya kamata Malami ya yi bayani dalla-dalla yadda wadanda basu san kan shari’a ba zasu gane. “Maganar da ya yi ba ta fadada ba musamman bayan ganin yadda aka afka har gidan Igboho aka halaka mutane cikin dare.

“A bayyane yake, rayuwar Igboho ake farauta. Don haka wacce doka Igboho ya karya bayan an afka gidan sa? Malami ya yi wa ‘yan Najeriya bayani.”

Related posts

Leave a Comment