Dalilan Da Ya Sa Gwamnatin Tarayya Dakatar Da Shirin Janye Tallafin Mai

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar bayanai su na zuwa a game da yadda shawarwarin tsaro suka tursasa gwamnatin Muhammadu Buhari ta lashe aman da tayi a kan tallafin fetur.

An ruwaito shugaban kasa Muhammadu Buhari ya hakura da maganar janye tallafin man fetur bayan ya yi la’akari da wasu shawarwari da ya samu.

Bayanan da jami’an tsaro suka ba Mai girma shugaban kasa shi ne za a barke da zanga-zangan da ya fi na EndSARS kamari idan har farashin man fetur ya tashi.

Wani jami’i da ya zanta da jaridar Punch ya ce da farko Muhammadu Buhari ya yi niyyar dabbaka sabuwar dokar IPA wanda zai jawo litar man fetur ya kara tsada. Jami’in da bai bari a kama sunansa ba ya ce gwamnatin tarayya ta ji tsoron ‘yan adawa su yi amfani da wannan zanga-zanga, su kawowa APC matsala a 2023.

Rahoton da aka kai wa shugaban kasa “’Yan sanda, DSS, NIA da ofishin NSA su kan aika rahoton tsaro ga shugaban kasa a game da abubuwa irinsu tallafin man fetur.” “Rahoton da aka aikawa shugaban kasa ya nuna kungiyoyi su na shirin yin zanga-zangar da ya nunka na EndSARS kusan sau goma.”

“Ana hasashen litar man fetur zai tashi zuwa N350 idan farashi ya cigaba da tashi a kasuwar Duniya. Hakan zai jawo zanga-zanga.”

“Sun kuma jawo hankalin shugaban kasa a kan juyin-mulkin da ake ta yi a kasashen Afrika da yadda ‘yan adawa ke amfani da damar.” “Wannan ya sa shugaban Najeriya ya dakatar da cire tallafin, ya bar wa duk gwamnatin da za ta zo wannan nauyi.”

Related posts

Leave a Comment