Tsohon Kwamishinan Aiyuka da Gine-gine, Muaz Magaji “ya kurumce” bayan wani hatsari da ya rutsa da shi lokacin da ?an sanda su ka taso shi za su kama shi a Abuja a jiya Alhamis, kamar yadda lauyansa ya shaidawa Kotun Majistare a Jihar Kano.
An cafke Magaji ne bayan da garin gujewa kamu ya ci karo da fitilar kan titi a motarsa.
Da yake baiyana gaban Alkalin Kotun, Aminu Gabari a yau Juma’a, Lauyan Magaji, Gazzali Ahmad, ya ce wanda yake karewa ya rasa ji na ?an wani lokaci sakamakon raunin da ya samu bayan fitar da jakar iska ta yi a motarsa.
Ahmad ya ?ara da cewa wanda ake tuhumar ba zai iya sauraron tuhume-tuhumen da ake masa balle ya amsa ko akasin haka.
Don haka lauyan ya ro?i kotu da ta bayar da belin wanda yake karewa domin nemar masa lafiya a asibiti.
Da yake yanke hukunci kan bu?atar lauyan, Gabari ya ba da umarnin a kai Magaji asibitin shalkwatar ‘yan sanda kuma ya ci gaba da zama a hannun ‘yan sanda.
Sai Gabari ya ?age sauraron ?arar zuwa ranar Litinin, 31 ga watan Janairu.
