Da Wuya A Yi Nasara A Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa – Shugaban Kasa

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis, ya bayyana cewar yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya ya zama mai matukar wahala.

Shugaban na Najeriya ya bayyana hakan ne a lokacin da yake magana a wani taro tare da shugabannin kudu maso gabas a Owerri yayin ziyarar aiki na kwana daya da ya kai jihar Imo.

Kakakin shugaban kasa, Femi Adesina, ya nakalto shugaban kasar a cikin wata sanarwa a shafin Facebook yana mai cewa babu wanda zai tuhume shi da mallakar kamfanoni ko manyan gidaje a ko ina cikin kasar nan.

Buhari wanda ya rage masa kasa da shekaru biyu ya kammala wa’adin mulkinsa na biyu ya ce idan ‘yan kasa suka samu tsaro, za su damu da harkokin gabansu ne.

Yayin da yake bayyana cewa zai yi duk abin da zai iya don ganin ‘yan Najeriya masu aiki tukuru sun yi nasara a cikin ayyukan su, shugaban kasar ya ce zai ci gaba da kokarin barin gado na gaskiya da rikon amana a cikin tsarin.

“Babu wanda zai zarge ni da mallakar kamfanoni ko manyan gidaje a ko’ina cikin kasar nan kuma ina godiya ga Allah da na yi kokarin tsaftace kaina yadda ya kamata, don kada a yi garkuwa da ni. “Zan yi iya bakin kokarina don ganin ‘yan Najeriya da ke kokari, sun yi nasara a kokarin da suke yi.”

Related posts

Leave a Comment