Babu Gaskiya A Batun Zan Yi Takarar Gwamna 2023 – Malami

Ministan Shari’a a tarayyar Najeriya Abubakar Malami ya fito ya nesanta kanshi daga labaran da ke yawo a biranen Jihar Kebbi na cewar wai zai fito takarar Gwamnan Jihar Kebbi a shekarar za?e ta 2023 dake tafe.

Mai magana da yawun Ministan Shari’an Jibrilu Gwandu ya sanar da hakan, a cikin wata takardar sanarwa da ya sanyawa hannu kuma aka rarraba ta ga manema labarai a birnin Kebbi.

“An janyo hankalinmu zuwa ga wani rahoton karya da ke ikirarin cewa fastocin Atoni Janar na tarayya kuma ministan shari’a na neman kujerar gwamna a zaben 2023 sun cika ko ina a jihar.
“Mun karade birnin tare da ‘yan jarida, sun gani da idanunsu cewa babu kamshin gaskiya a rahoton. Bamu ga kowace fosta makamancin haka ba a Birnin Kebbi.
“Don haka, muna so jama’a su yi watsi da wannan labari saboda hasashen mawallafin ne kawai,” in ji shi.

Jibrilu-Gwandu ya bayyana cewa ministan na da magoya baya da dama a jihar da ka iya nuna ra’ayi a kansa, saboda taimakon al’umma da alkhairinsa, inda ya kara da cewa labarin fastocin kamfen dinsa ba komai bane face kanzon kurege.

“A yanayi da wani zai shirya karairayi da sunan aikin jarida yana bata sunan aikin ne.
“Idan kun tuna, a ranar 16 ga watan Maris, 2020, Malami ya bukaci magoya bayansa da su janye daga batun kamfen din neman takarar gwamnansa na 2023, domin lokaci bai yi ba na kamfen din siyasa kamar yadda yake a dokar zabe na kasa,” in ji shi.

Related posts

Leave a Comment