Honorabul Abdulmumini Jibrin, zababben dan majalisa daga Jihar Kano jigo a tafiyar Kwankwasiyya ya ce, da izinin gwamna Abdullahi Umar Ganduje zababben shugaban kasa, Bola Tinubu ya gana da sanata Rabiu Musa Kwankwaso a Faransa.
A baya, rahotanninmu sun bayyana yadda Kwankwaso da Tinubu suka shafe sa’o’i hudu suna muhimmiyar ganawa a ranar Litinin din da ta gabata a kasar Faransa.
Ganduje dai ya nuna damuwa game da ganawar tasu, inda yace Tinubu ya gana da Kwankwaso ne don neman madadi.
A wani faifan muryar da aka yada, an ji Ibrahim Masari da Ganduje suna magana, inda yace Tinubu ya gana da Kwankwaso, lamarin da bai masa dadi ba.
Sai dai, a wata tattaunawa da Daily Trust, Jibrin, wanda ke cikin wadanda suke tare da Ganduje a Faransa, ya ce Ganduje ya tabbatar masa cewa, Tinubu ya shawarce shi kafin ganawa da Kwankwaso.
“Kamar dai kowanne dan Najeriya, na kadu da sauraran faifan muryar amma ina tunanin abu mafi muhimmanci shine ina son tabbatar muku cewa an sanar da gwamna Ganduje. “Kuma shi da kansa ya tabbatar min, ya sanar dani balo-balo cewa zababben shugaban kasa ya gayyace shi kuma ya fada masa cewa yana shirya ganawa da Kwankwaso kuma ya tambayi Ganduje ko yana da ja, kuma Gandujen dai ya shaida min ya cewa zababben shugaban kasa bashi da ja.”
Da yake karin haske game da yadda faifan muryar ke yaduwa, ya ce sam ba a yiwa Bola Tinubu adalci ba na bayyana shi a matsayin mayaudari. Ya kara da cewa: “Don haka ba daidai bane a ga laifin zababben shugaban kasa a bainar jama’a daga bakin Ganduje wanda ya san tabbas cewa shugaban ya nemi shawarinsa kafin ganawar saboda ya tabbatar min da hakan a bayyane.
