?ungiyar likitoci da aka fi sani da NARD a ta?aice, ta tsagaita yajin aikin gama garin da take yi na tsawon makonni shida domin bai wa Gwamnatin Tarayya damar biya mata bu?atunta.
A jiya Litinin NARD ta ba da sanarwar tsagaita yajin aikin da ta shafe kwanaki 64 ta na yi, kamar yadda shugaban ?ungiyar na ?asa, Dr Godiya Ishaya, ya bayyana a tattaunawar da Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ya yi da shi a Abuja.
Ishaya ya ce ?ungiyar ta ?auki matakin tsaigaita yajin aikin ne duba da ?o?arin da ta ga gwamnati na yi don cimma bu?atunta.
Ya ce muddin gwamnati ta iya cimma bu?atunta cikin makonni shida da ta ?ibar mata, ka iya yiwu ta janye yajin aikin nata baki ?aya.
A cewar Ishaya, “Ba wai mun janye yajin aikin ba ne baki ?aya, mun tsagaita ne na makonni shida don bai wa gwamnati damar yin abin da ya dace.
“Idan gwamnatin ta iya aiwatar da abin da ya kamace ta a cikin makonni shida, daga nan za mu zauna mu duba mu ga mataki na gaba da ya dace mu ?auka.
“A farkon wannan shekara aka cimma yarjejeniya tsakanin NARD da Gwamnatin Tarayya, rashin aiwatar da yarjejeniyar ya sa muka tsunduma yajin aiki.”
Kazalika, Ishaya ya ce ?o?arin da suka ga gwamanti na yi a yanzu wajen bai wa yarjejeniyar da ke tsakani muhimmanci, ya sa shugabannin ?ungiyar suka yi taron gaggawa inda a nan suka cimma matsayin sassauta matakin yajin aikin nasu.
Bu?atun da NARD ta nema a wajen gwamnati sun ha?a da; biyan da ?arin alawus-alawus da kashi 50 ga ma’aikatan kiwon lafiya, da biyan bashin alwus na ya?i da cutar korona da suke bi, da biyan inshorar ma’aikatan da suka rasa ransu a bakin aiki a dalilin ya?i da cutar korona da dai sauransu.
Tun bayan da likitocin suka soma yajin aiki a watan Agustan da ya gabata, asibitocin gwamnati a matakin tarayya da jihohi suka shiga garari saboda rashin likitocin da za su kula da marasa lafiya.
