Labarin dake shigo mana daga Fadar mai alfarma Sarkin Musulmi Dr Sa’adu Abubakar na bayyana cewar gobe Alhamis 30 ga Watan Yunin 2022 shi ne 1 ga watan Dhul Hijjah 1444.
Za a yi hawan Arfa a ranar juma’a 9 ga watan Dhul Hijjah sannan Sallah za ta kasance ranar Asabar idan Allah ya kaimu.
Mai Alfarma Sarkin Musulmi ya bukaci jama’a su raya kwanaki 10 na farkon Dhul Hijjah domin dacewa da rahama.
