Da Dumi-Dumi: Da Yiwuwar ASUU Ta Sake Tsunduma Yajin Aiki

Akwai yiwuwar a sake tafiya yajin aiki bayan da ?ungiyar Malaman Jami’o’i, ASUU ta baiwa gwamnatin tarayya wa’adin makonni uku a yau Litinin da ta cika al?awuran da ta ?auka.

Wannan na zuwa ne bayan da ?ungiyar Manyan Ma’aikata na Jami’o’i da kuma ta Ma’aikatan da ba samu koyarwa ba na jami’o’i su ka gana a yau domin ?aukar mataki na gaba a kan rashin cika al?awuran da gwamnatin tarayya ta yi a kan bu?atunsu.

A bara ne dai Gwamnatin Tarayya ta sanya hannu a kan yarjejeniyar biyan ha??o?in ?ungiyoyin.

Da ya ke ganawa da manema labarai a Abuja, shugaban ASUU ?in na ?asa, Farfesa Emmanuel Osodeke, ya nuna rashin jin da?insa a bisa yadda gwamnati ta ?i cika musu al?awuran da ta ?aukar musu.

“Mun baiwa gwamnatin tarayya wa’adin makonni uku. Idan makonni ukun su ka cika ba a biya mana bu?atun mu ba, to ba makawa za mu tafi yajin aiki.

“Ai mun yi ?o?ari da mu ka basu isasshen lokaci amma har yanzu shiru,” in ji shi.

Related posts

Leave a Comment