‘Yan Bindiga Sun Hallaka Mutum 28 A Kudancin Kaduna

Mutum 28 sun mutu, an jikkata wasu da dama a harin ?an bindiga a kauyukan Malagum 1 da Sokwong na Karamar Hukumar Kaura ta Jihar Kaduna.

Jaridar Aminiya ta rawaito cewa Sakataren Karamar Hukumar, Raymond Ibrahim, ya ce ?an bindiga sun far wa kauyen Sakwong ne da misalin karfe 12 na dare kafin wayewar garin Lahadi, su na harbi kan mai uwa da wabi tare da cinna wa gidade da dukiyoyi wuta.

Ya ce, “Da safen yau muka dawo daga wurin muka ga gawarwaki tara, daga nan muka karasa zuwa kauyen Malagum 1 inda ganau suka tabbatar mana cewa an kashe mutum 19.”

Raymond Ibrahim ya ce an kai harin ne kwana biyar bayan wani da aka kai a Malagum 1 aka kashe mutum hudu.

Related posts

Leave a Comment