Da Dumi-Dumi: An Amince INEC Ta Aike Sakamakon Zabe Ta Yanar Gizo

Bayan jan kafa na wani tsawon lokaci da matsin lamba, yanzu majalisar dattawan Najeriya ta amince hukumar za?e mai zaman kanta ta INEC ta yi amfani da na’ura domin aika sakamakon za?e.

Majalisar ta sauya ra’ayinta na farko inda ta ?i amincewa da matakin game da tura sakamakon za?e daga muza?u ta hanyar intanet.

A zaman da ta yi na ranar Talata, majalisar dattawan ta ce INEC za ta iya amfani da na’ura ta aika sakamakon za?e a lokacin da ya dace idan har hukumar kula da harakokin sadarwa ta Najeriya NCC ta amince.

Majalisar ta kuma ka?a kuri’ar amincewa da tsarin gudanar da za?en fidda ?an takara na jam’iyyu ta hanyar za?e kai tsaye tare da sa idon hukumar INEC.

Related posts

Leave a Comment