Da ?umi-?umi: An Cafke Sowore A Abuja

Jami’an tsaro a Abuja sun cafke gawurtaccen dan tada zaune tsayen nan Omoyele Sowore mai gidan jaridar Sahara Reporters wadda ta kware wajen cin zarafin al’ummar Arewa a birnin tarayya Abuja.

Hakazalika, kamar yanda Sahara suka wallafa, an ji masa ciwo kafin a yi nasarar cafke shi tareda sauran abokanansa.

Idan dai baku manta ba, Omoyele Sowore yana daya daga cikin matasa da suka shirya zanga-zangar ENDSARS, wadda ta janyo asarar rayukka da dimbin dukiya a Arewacin Najeriya da kuma Kudanci.

Hakazalika, Omoyele Sowore ya sha yin ikirarin yi wa buhari zanga-zanga domin ganin an ham?arar da gwamnatinsa kamar yanda ya sha rubutawa a shafukansa na sada zumunta.

Kama Sowore dai na zuwa ne a daidai lokacin da masu adawa da gwamnatin Buhari ke cigaba da sukan Shugaban na take ha??in bil adama da haramta wa jama’a sukar manufofin gwamnatin.

Related posts

Leave a Comment