CORONA: Dole A Dakatar Da Bu?e Makarantu A Yanzu – Majalisa

Majalisar dokoki ta ?asa ta nemi Gwamnatin tarayya ta dakatar da batun komawar dalibai Makarantu har zuwa nan da watanni uku masu zuwa, domin ganin abin da ka iya zuwa ya dawo akan batun ya?i da cutar CORONA.

Shugaban kwamitin, Julius Ihonvbere, ya ce gwamnatin tarayya ba ta tuntu?i sauran masu ruwa da tsaki kafin ta bada sanarwar komawar dalibai makarantu ba.

Kwanan watan bu?e makarantu na ranar Litinin,18 ga watan Junairu, ya jawo cece-kuce sakamakon gaggawar shawarar da gwamnatin tarayya ta yanke, inda suka ce akwai ha?ari a bude makarantu saboda Annobar COVID-19.

Da yake maida martani akan bu?e makarantu ranar 18 ga watan Junairu, Honarabul Julius Ihonvbere, shugaban kwamitin majalisa akan ilimi yace bu?e makarantu babbar barazana ce ga ya?i da annobar COVID-19 a karo na biyu.

Ihonvbere ya ce Gwamnatin Tarayya bata tuntu?i majalisa ba kafin yanke shawarar cewa dalibai zasu kara komawa makarantu ranar 18 ga wata ba.

Ya ?ara da cewa a dakatar da komawa makarantun zuwa nan da watanni uku don ganin yadda hali zai yi, ya kuma koka akan rashin “daukar mataki ko wani shirin kare ?alibai daga annobar COVID-19.

“Duk da kasancewar makarantu a rufe suke, ana samun mutane 500 zuwa 1000, ina kuma ga ace an bu?e makarantu. “Akan me ake gaggawar bu?e makarantu ba tare da daukar matakan kariya ko wani shiri akan kare rayuwar ?a’?anmu ba?

“Basu tuntu?e mu ba, ya kamata a?alla ace sun tuntu?i kwamitin mu, ba wanda ya tuntu?emu koda daga ma’aikatar ilimi ne,” a cewar Dan majalisar.

Related posts

Leave a Comment