Katin Zama ?an ?asa Zai Shafi Har ‘Yan ?asar Waje – Pantami

A ranar Asabar din da ta gabata ne Gwamnatin Tarayya ta ba da umarnin rufe hedkwatar Hukumar Kula da Shaidun Dan Kasa da ke babban Birnin Tarayya Abuja.

Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na zamani, Dakta Isa Ali Ibrahim Pantami, wanda ya ba da wannan umarni, ya kuma umarci Hukumar NIMC da ta bude wurare 20 a cikin Babban Birnin Tarayya, kamar yadda aka kara a sauran jihohi, domin dakatar da cincirindon jama’ar da ke taruwa a hedikwatar hukumar a kowacce rana da zimmar samun katin shaidar zama dan kasa.

Haka zalika ministan ya bada umurnin a yiwa dukkannin ‘yan kasashen waje dake zaune a Najeriya rijistar zama dan kasa.

Sanarwar ta ce a ranar Talata ne 19 ga Janairun wannan watan za a samar da wurin aikin yin rijistar a ma’aikatar harakokin waje.

Ministan ya ce lambar ta sheda wajibi ce ga ‘yan kasashen waje da za su shafe shekara biyu ko fiye a kasar.

Related posts

Leave a Comment