?ungiyar Malaman Jami’o’i ta ?asa, ASUU ta yi barazanar maka Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje a kotu, matu?ar bai dawowa da jami’ar Yusuf Maitama Sule Kano, gine-ginen ta da ya kar?e da kuma filayenta da ya sayar ba.
ASUU, reshen Jami’ar Yusuf Maitama Sule, wacce jami’ar gwamnati ce, ta yi wannan barazana ne a wata sanarwa da shugabanta, Dakta Abdulraza? Ibrahim ya sanyawa hannu, ya kuma rabawa manema labarai a ranar Asabar.
A sanarwar, ASUU ta zargi Ganduje da kar?e wasu muhimman gine-gine da su ka ha?a da Sashin Koyar da Likitanci da ke Kwanar Dawaki da kuma Cibiyar Koyar da Harkokin Kasuwanci da ke ?aramar Hukumar Dawakin Tofa.
Bugu-da-?ari, ?ungiyar ta zargi Ganduje da sayarwa da rarraba filaye mallakarta a Babban Sashen jami’ar da ke titin Muhammadu Buhari.
ASUU ta yi ?orafin cewa, shi wannan Sashen Koyar da Likitancin da Ganduje ya kar?e, ya tilastawa ma’aikata da ?aliban wajen tashi da kuma yin karere a wasu ?angarori na jami’ar.
Ta kuma yi kukan cewa ?aliban sashen na wahala wajen jigilar zuwa ?aukar darasi tsakanin ?angarorin jami’ar.
Haka-zalika, ?ungiyar ta koka da cewa kar?e Sashen Koyar da Harkokin Kasuwanci da gwamnatin Ganduje ta yi a Dawakin Tofa ya rushe Karatun Shiga Jami’a, IJMB da kuma koyar da harkokin kasuwanci a jami’ar.
ASUU ta ?ara kokawa da cewa irin wannan kar?e gine-ginen da kuma sayar da filayen jami’ar zai kawo mata na?asu a wajen ci gabanta.
Sabo da haka, ASUU ?in ta yi kira ga Ganduje da ya tsaya da saide-saiden filaye da kar?e-kar?en gine-gine a jami’ar.
Sannan ta yi kira ga gwamnan da ya gaggauta dawo da wa?anda ya kar?e ya kuma sayar, in da ta ce, in ba haka ba, ba ta da wani za?i illa ta maka shi a gaban ?uliya.
