Ministan ya?a labarai da al’adu Lai Mohammed, ya ce Shugaban ?asa Buhari ya yi rawar gani sosai wajen shawo kan matsalar tsaro da karya laggon Boko Haram a yankin Arewa maso gabashin Najeriya, al’ummar Arewa maso gabas sun daina biyan ‘yan Boko Haram haraji, suna rayuwa cikin walwala da kwanciyar hankali. Lai Mohammed ya bayyana hakan ne a ganawarsa da kungiyar masu kamfanonin jarida a Najeria NPAN a Legas ranar Alhamis, akan matsalar tsaro a Najeriya musamman yankin Arewacin Najeriya. Lai Mohammed yace kwace garuruwan da ‘yan Boko Haram ke…
Read MoreCategory: Tsaro
Tsaro
Matsalar Tsaro: Buhari Ya Amshi Goron Gayyatar Majalisa
Shugaban ?asa Muhammadu Buhari ya amince da zama da ‘yan majalisar wakilai don tattaunawa a kan matsalar rashin tsaro, kamar yadda ‘yan majalisar suka bukata. Kamar yadda kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila yace, an tsayar da ranar da za a tattauna, kuma nan kusa za a sanar da lokacin. Ya fadi hakan a ranar Laraba, inda yace Shugaban kasa ya fi kowa shiga cikin damuwa a kan yanayin rashin tsaron da kasarsa take ciki, kuma zai yi wa ‘yan Najeriya magana ta wurin wakilansu nan kusa. Shugaban kasa ya yanke…
Read More?aukar Fansa: Sojoji Sun Hallaka Kwamandojin Boko Haram Masu Yawa
Dakarun sojojin Nijeriya sun fara daukar fansar jinin ‘yan Nijeriya akan ‘yan ta’addan Boko Haram. Wato jama’a kamar yadda hedikwatar tsaron Nijeriya ta fitar da sanarwar cewar dakarun sojojin Nijeriya sun hallaka jagororin ‘yan Boko Haram a cikin dajin Sambisa dake kan iyakar Nijeriya da kasar Kamaru da Chadi ta jihar Borno. Majiyar mu ta tabbatar mana da cewa dakarun sojojin Nijeriya sun lalata sansanonin ‘yan Boko Haram tare da hallaka kwamandojin su a cikin dajin Sambisa. Majiyar mu ta ci gaba da bayyana mana cewa tabbas dakarun Sojojin Nijeriya…
Read MoreKisan Zabarmari: Ba Zamu Lamunci Kisan Talakawa Ba – Matasan Arewa
Hadakar kungiyar Matasan Arewa maso gabashin Najeriya sun fusata damn tin Allah wadai, ganin yadda yan’ta’adda suka kashe rayukan manoma 43 a kauyen Zabarmari a jihar Borno, da kuma harsashen alkalman zasu fi haka kawo Iyan yanzu. Matasan sun shaida wa manema labarai a daren jiya laraba a lokacin da suke zantawa da yan’ jaridar kan wan nan batu na kisan gillar, da kuma kiran gwamnatin tarayya da ta tabbatar da aiwatar da shawarwarin gwamna Zulum na jihar Borno Shugaban kungiyar Matasan Barrista Hussaini Saraki, da ya jagoranci mambobinsu yana…
Read MoreMatsalar Tsaro: Ina Zargin Buhari Ya Samu Ta?in Hankali – Ezikwesili
Tsohuwar Ministar ilmi, Madam Oby Ezekwesili ta nuna shakkunta game da lafiyar ?wa?walwa ta shugaban ?asa Muhammadu Buhari. Rahotanni sun ce Madam Oby Ezekwesili ta bukaci ayi wa lafiyar kwakwalwa da jikin shugaban kasa Muhammadu Buhari binciken kwa-kwaf. Tsohuwar ‘yar takarar shugaban kasar ta bukaci ayi wannan ne domin al’ummar Najeriya su san ko shugaban kasar na su ya na da koshin lafiya. A cewar Oby Ezekwesili, halin da ake ciki yanzu a Najeriya na rashin tsaro, ya ci ace an tashi an san lafiyar shugaban kasa Muhammadu Buhari.“Ina tunani…
Read MoreDalilan Da Ya Sa Muka Yanyanka Manoma A ?auyen Zabarmari – Boko Haram
Kungiyar Boko Haram ta fitar da wani faifen bidiyo da take bayyana cewa ita ke da alhakin kai hari tare da hallaka manoman shinkafa fiye da 40 a kauyen Kosheba da ke Zabarmari a jihar Borno da ke arewa maso gabashin kasar. Ta kuma ce ta hallaka manoman ne saboda sun kama wasu dakarunta inda suka mika su a hannun sojojin Najeriya da ke gudanar da aiki a yankin. Da ma dai tun bayan da aka kai harin mutane da dama suka fara zargin cewa mayakan na Boko Haram ne…
Read MoreRashin Tsaro: Majalisar Wakilai Ta Nemi Buhari Da Gurfana Gabanta
‘Yan Majalisar wakilan Tarayyar Najeriya a zamansu da suka yi ranar Talata, sun amince da gayyatar Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana gabansu don yi musu bayani game da halin rashin tsaro da ake ciki a kasar nan. An zartar da kudurin ne bayan wata takaddamar da ta kunno kai a yayin muhawara kan kudirin “Bukatar Gaggawa da bincike kan kisan manoman da basuji-basugani ba a Karamar Hukumar Jere ta Jihar Borno”, Wadanda suka mika bukatar gayyatar shugaba buhari sun hada da Hon. Ahmed Satomi, Hon. Mohammed Tahir Monguno, Hon. Zainab…
Read MoreMatsalar Tsaro: Majalisa Ta Nemi Buhari Ya Kori Shugabannin Tsaro
Majalisar Dattawa ta bukaci Shugaba Muhammadu Buhari ya sallami Manyan Hafsoshin Tsaron Najeriya saboda gazawar da suka nuna. Majalisar ta yi kiranta ne bayan bukatar hakan da Sanata mai wakiltar Borno ta Tsakiya, Kashim Shettima ya gabatar a lokacin zamanta na ranar Talata. Sanatocin sun sha aikewa da makamanciyar bukatar ta maye gurbin hafsoshin tsaron da sabbin jini masu fikirar dakile ayyukan ta’addanci a fadin Najeriya, sai dai bukatar ta su ba ta samu karbuwa ba. An shafe shekaru bangarori da dama na Najeriya na kira ga Buhari ya sallami…
Read MoreLalacewar Tsaro: Ya Wajaba Buhari Ya Sauka – Dr Gumi
Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan a Najeriya, Shaikh Ahmad Abubakar Gumi ya bukaci Shugaba Buhari ya yi murabus tunda ya kasa tsare rayukan al’umma. Kiran Shaikh Gumi na zuwa ne bayan kisan gillar da ’yan Boko Haram suka yi wa manoma 43 a garin Zabarmari da ke Jihar Borno. Malamin ya ce kashe-kashen da ake yi a Gwamnatin Buhari ya ninka na gwamnatin da ta gabata, don haka babu wani uzuri da za a ci gaba da yi wa gwamnatin. Shaikh Ahmad Gumi ya koka kan yadda ya ce kullum…
Read MoreLalacewar Tsaro: Ya Wajaba Buhari Ya Sauka Daga Mulki – Dr Gumi
Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan a Najeriya, Shaikh Ahmad Abubakar Gumi ya bukaci Shugaba Buhari ya yi murabus tunda ya kasa tsare rayukan al’umma. Kiran Shaikh Gumi na zuwa ne bayan kisan gillar da ’yan Boko Haram suka yi wa manoma 43 a garin Zabarmari da ke Jihar Borno. Malamin ya ce kashe-kashen da ake yi a Gwamnatin Buhari ya ninka na gwamnatin da ta gabata, don haka babu wani uzuri da za a ci gaba da yi wa gwamnatin. Shaikh Ahmad Gumi ya koka kan yadda ya ce kullum…
Read MoreAn Ragewa Babban Soja Mu?ami Dalilin Fallasa Asirin Boko Haram
Kotun Sojoji mai tuhumar jami’an ta a asirce, ta yanke wa Manjo Janar Olusegun Adeniyi hukuncin rage masa mukami, inda aka maida shi baya tsawon shekaru uku, hukuncin na nuni da cewa sai nan da shekaru uku Adeniyi zai sake kai mukamin da ya ke a yanzu. An yanke masa hukuncin ne saboda ya fito a soshiyal midiya ya fitar da bidiyon da ake nuna shi ya na korafin rashin wadatattu da ingantattun kayan fada da sojojin Nigeria ba su da shi a fagen yaki da Boko Haram, balle har…
Read MoreKatsina: ‘Yan Bindiga Sun Yi Wa Manoma Yankan Rago
‘Yan ta’addan sun yi wa manoma har guda bakwai yankan rago har lahira a cikin karamar hukumar Sabuwar jihar Katsina. Dan Majalissar dokokin jihar Katsina mai wakiltar mazabar Sabuwa Hon Ibrahim Kaka Machika shi ne ya tabbatar da faruwar lamarin a zauren majalissar a jiya Litinin. Dan Majalissar ya ce daga cikin wadanda yan bindigar suka yanka har da wata uwa mai shayarwa. Lamarin ya afku ne a kauyen Tashar Bama, da Dogun Muazu da kuma Unguwar Maigayya dake karamar hukumar sabuwa dake jihar katsina. Ko a karanar hukumar faskari…
Read MoreAiki Muka Za?eka Ka Yi Ba Surutun Allah Wadai Ba – Sheikh Nuru Ga Buhari
Fitaccen Malamin addinin nan na garin Abuja, Sheikh Muhammad Nuru Khalid ya yi martani game da tabarbarewar tsaro a Gwamnatin Buhari. Anga wani bidiyo inda fitaccen Malamin yake cewa “Zamu shiga Internet mu fadawa duniya, ba zamu iya yin shiru a yanayin da ake ciki ba ana ta kashe mu kamar kiyashi ba wanda zai yi magana.” “Anan wajen na taba fada nace wallahi kajin gonarsu baka isa kayi masu irin wannan kisan ba, ba gonar [babban] dan Nigeria da zaka je ka kashe kaji 200 haka kawai in ba…
Read MoreTsaro: Sojojin Najeriya Ihu Bayan Hari Suke Yi – El Rufa’i
Gwamna Nasir El-Rufai na Jihar Kaduna ya ce shi da sauran gwamnoni “hannunsu a ?aure yake” game da yadda ake gudanar da harkokin tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma a jihohinsu. Gwamnan na magana ne ta cikin shirin Politics Today a kafar Channels TV a yammacin yau, yana mai cewa ba su da wani iko mai yawa. “Hannuna a ?aure yake a jihata. Gwamnoni da yawa hannunsu a ?aure yake. Ana kiranmu shugabannin tsaro (chief security officers) a suna kawai amma ba mu da wani iko kan manyan abubuwa…kusan babu yadda…
Read MoreBoko Haram: Tun Da Sojin Najeriya Sun Gaza A Yi Hayar Sojoji Daga Waje – Zulum
Gwamnan jihar Barno Babagana Zulum ya shawarci tawagar gwamnatin tarayya da suka kawo masa jaje, da yi masa ta’aziyyar kisan gillan da Boko Haram suka yi wa manoma sama da 40 a kauyen Zabarmari. Tawagar gwamnatin Tarayya ta isa garin Maiduguri ranar Litini sannan sun gana da gwamnan jihar Babagana Zulum. Daga nan sai sai suka ziyarci garin Zabarmari domin yi wa mutane da iyalan mamatan ta’aziyya. A jawabinsa Zulum ya shawarci gwamnatin tarayya ta yo hayan zaratan sojoji daga kasashen waje su zo su gama da Boko Haram tunda…
Read MoreBorno: Boko Haram Ta ?one Gari Da Karkashe Mutane A Damboa
A ?alla masu saran itace 13 ne suka mutu, baya ga kone garin Kareto da ’yan Boko Haram suka yi a jihar Borno a karshen mako. ’Yan ta’addar sun kone garin Kareto ne a ranar Juma’a tare da kone wasu sabbin gidaje da gwamnatin jihar ta gina wa ’yan gudun hijira. Bayanai sun nuna cewa harin ya faru biyo bayan shirye-shirye da jihar ke yi na mayar da wasu ’yan gudun hijira zuwa garin. Garin Kareto da ke Karamar Hukumar Mobar a Jihar Borno, shi ne garin da gwamnan jihar…
Read MoreKisan Zabarmari: Laifin Manoman Ne – Garba Shehu
Kakakin Shugaban kasa Muhammad Buhari, Malam Garba Shehu a wani martani da yake mayarwa game da kazamin harin da aka kai kauyen Zabarmari dake karamar hukumar Jere ta Jihar Borno, Ya ce ai suma Manoman ya kamata su tabbatar da ingancin tsaron gonakin su a wajen Jami’ai kafin su shiga gonakin su. Kazalika Malam Garba Shehu, ya kara jaddada cewar kada Al’ummar Najeriya su raina aikin Jami’an tsaro da Jagorancin Shugaban kasa Muhammad Buhari, a fannin bayar da ingancin tsaro a kasar nan, musamman a yankin Arewa maso gabashi. Garba…
Read MoreKisan Manoma: Buhari Ya Aike Tawaga Borno
Wata tawaga ta gwamnatin tarayya bisa ga umarnin mai girma Shugaban ?asa Muhammadu Buhari karkashin jagorancin Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, sun isa garin Maiduguri, babbar birnin jihar Borno. Tawagar sun kai ziyarar jaje da ta’aziyya ne a kan kisan kiyashin da mayakan Boko Haram suka yi wa manoma 43 a yankin Zabarmari da ke karamar hukumar Jere ta jihar. An tattaro cewa manyan jami’an gwamnatun sun isa garin Maiduguri a ranar yau Litinin, 30 ga watan Nuwamba, domin sauke nauyin gabatar da ta’aziyar ga ‘yan uwan mamatan da kuma…
Read MoreJama’ar Borno Na Kawo Cikas Wajen Samar Da Tsaro – Rundunar Soji
A ranar Litinin, rundunar sojin Najeriya ta nuna takaicin yadda wasu ‘yan arewa maso gabas suke kin bai wa jami’an tsaro bayanai wadanda za su taimaka wurin bincike da gano ‘yan ta’adda. Kakakin rundunar sojin, manjo janar John Enenche, ya bayyana a gidan talabijin na Channels inda yace abubuwan da ke kawo tabarbarewar tsaro har da yadda mazauna yankuna suke kin bayar da bayanai wadanda za su taimaki sojoji. “Wannan shine damuwarmu. Yana matukar damun mu, muna bukatar bayanai, su ne mazauna yankunan, idan sun ga wata matsala ta barke,…
Read MoreZabarmari – Da Gangan Sojoji Suka Bari Aka Yi Wa Manoma Yankan Rago – Salihu
Mazauna garin Zabarmari sun sanar da sojoji game da harin da aka kai masu amma babu abunda aka yi, kamar yadda suka bayyana a ranar Lahadi, 29 ga watan Nuwamba. An ruwaito cewa wani mazaunin kauyen da ya tsira, wanda ya bayyana sunansa a matsayin Abubakar Salihu, ya bayyana cewa sun hango hatsarin bayan sun kama wani dan Boko Haram sannan suka mika shi ga jami’an tsaro. “Mun sanar da sojoji cewa Jama’armu sun gano yan Boko Haram da yawa amma babu abunda aka yi game da hakan.“Ranar bakin ciki…
Read More