Rashin Tsaro: Majalisar Wakilai Ta Nemi Buhari Da Gurfana Gabanta

‘Yan Majalisar wakilan Tarayyar Najeriya a zamansu da suka yi ranar Talata, sun amince da gayyatar Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana gabansu don yi musu bayani game da halin rashin tsaro da ake ciki a kasar nan.

An zartar da kudurin ne bayan wata takaddamar da ta kunno kai a yayin muhawara kan kudirin “Bukatar Gaggawa da bincike kan kisan manoman da basuji-basugani ba a Karamar Hukumar Jere ta Jihar Borno”,

Wadanda suka mika bukatar gayyatar shugaba buhari sun hada da Hon. Ahmed Satomi, Hon. Mohammed Tahir Monguno, Hon. Zainab Gimba, Hon. Muktar Betara, Hon. Mallam Bukar Gana, Hon. Haruna Mshelia, Hon. Ahmadu Usman Jaha, Hon. Ibrahim Mohammed Bukar, Hon. Usman Zannah, Hon. Abdulkadir Rahis.

Kisan Manoma 43 da Boko Haram ta yi a Zabarmari ya zama wani gagarumin labari da ya karade duniya, kuma ya yi matu?ar zubar wa gwamnatin Tarayya mutunci a idanun duniya, sannan ya nuna a fili raunin da bangaren tsaro ke fama da shi a kasar.

Bayan kisan da aka yi wa Manoman ne dai shugaban ?asa ya tura tawaga zuwa Jihar Borno domin jaje tare da bada umarni ga dakarun soji suyi dukkanin mai yiyuwa wajen gamawa da kungiyar Boko Haram.

Related posts

Leave a Comment