Sace ?aliban Kagara: Buhari Na Fuskantar Matsin Lamba Daga Waje

?ungiyoyin ?asashen duniya na ci gaba da matsa wa hukumomin Najeriya lamba, don ceto ?aliban nan su kusan 50, da masu satar mutane suka yi awon gaba da su daga wata makarantar Sakandire ta Kagara a jihar Neja. Da sanyin safiyar ranar Talata ne wasu ?an bindiga suka sace ?aliban da kuma wani malaminsu da iyalinsa shida mata da ‘ya’ya, a makarantar sakandiren garin Kagara da ke jihar Neja a arewacin Najeriya. A wannan karon hukumar kula da ?ananan yara ta Majalisar ?inkin Duniya wato UNICEF ta ce tana cike…

Read More

Matsalar Tsaro: Najeriya Na Dab Da Tarwatsewa – Tsohon Shugaban Kasa

Tsohon Shugaban ?asa na mulkin soja, Janar Abdulsalami Abubakar mai ritaya ya yi kakkausan gargadin cewa idan ba a gaggauta dakile hargitsi da tashe-tashen hankulan da ke faruwa a fadin kasar nan daban-daban ba, to Najeriya za ta iya tarwatsewa ba da dadewa ba. Haka Abdulsalami ya shaida wa manema labarai a ranar Laraba, a Minna, babban birnin jihar Neja. Wannan gargadi na shi ya zo ne kwanaki kadan bayan da aka kashe wasu Hausawa a Kasuwar Shasha da ke jihar Oyo. Duk da dai Hausawa ne zalla aka kashe…

Read More

Kisan ‘Yan Arewa Na Iya Haifar Da Basasa – ?ungiyar Arewa

?ungiyar cigaban Matasan Arewa wato Arewa Youth Forum (AYF) a takaice, ta yi kira da babbar murya ga Shugaban ?asa Buhari da ya yi gaggawar ?aukar mataki da?ile rikicin da ya kunno a sashin Kudancin kasar na kisan ‘yan Arewa, domin kawar da yiwuwar faruwar ya?in basasa a ?asar. Kungiyar ta bayyana hakan ne a cikin wata takardar sanarwa dake dauke da sa hannun Shugaban ?ungiyar Alhaji Gambo Ibrahim Gujungu, kuma aka rarraba ta ga manema labarai a Kaduna. Matasan sun bayyana cewar ba ?aramin kuskure ba ne furucin da…

Read More

Akwai Salihan Bayi Cikin ‘Yan Bindiga – Matawalle

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawallen Maradun ya ce ba duka tsagerun ‘yan bindiga bane mutanen banza, akwai bayin Allan mutanen ?warai a cikin su, wasu dole ce ta wajabta musu daukar bindiga. Gwamnan ya bayyana hakan ne ga manema labarai bayan ganawa da shugaba Buhari a fadar shugaban kasa ranar Alhamis, 18 ga Febrairu, 2021, inda ya ?ara da cewa yawancin ‘yan bindigan sun shiga harkar ne saboda irin rashin adalcin da al’ummar gari ke nuna musu. “Ba dukkansu bane mutanen banza. Idan ka bincike abinda ke faruwa, da kuma…

Read More

Akwai Siyasa A Matsalar Tsaro Da Najeriya Ke Ciki – Buratai

Tsohon hafsan Sojin Najeriya, Laftanan Janar Tukur Yusuf Buratai (mai murabus), ya bayyana cewar da akwai manyan kalubale da sha’anin tsaro ke fuskanta a kasar nan, wanda suka ha?a da Siyasa, bangaranci da sauransu, wanda hakan ke haifar da Cikas a kokarin da Gwamnati ke yi na yaki da ta’addanci a ?asar. Buratai ya yi wannan furuci ne a lokacin da ya bayyana gaban majalisar dokokin tarayya domin tantance shi a matsayin Jakada a ranar Alhamis, inda ya ce da yiwuwar wannan rikicin na Boko Haram ya cigaba har tsawon…

Read More

Ku Kare Kanku Daga ‘Yan Bindiga – Ministan Tsaro

Ministan Tsaron Nijeriya Manjo Janar Bashir Magashi mai ritaya, ya bukaci ‘yan Nijeriya su samu kwarin guiwar kare kansu daga hare-haren ‘yanbindiga da kasar ke fama da shi. Da yake magana da ‘yanjarida a ranar Laraba, kan aikin tantance sabbin shugabannin tsaro da majalisar wakilai ke yi, Magashi ya bayyana wadanda suka sace daliban da aka yi a makarantar sakandiren kimiyya ta Kagara a matsayin raggwaye. Ya ce ‘yan Nijeriya na da alhakin tabbatar da cikakken tsaro a tsakaninsu, yana mai yin watsi da ikirarin da wasu ke yi na…

Read More

Za Mu Yi Amfani Da Salon Katsina Wajen Ceto ?aliban Neja

Ministan tsaron Najeriya Janar Bashir Salihi Magashi mai ritaya, ya bayyana cewa hukumar Sojoji za ta yi amfani da dabarar da akayi amfani da ita wajen ceto daliban Kankara domin ceto daliban makarantar gwamnati dake Kagara, a jihar Neja. Bashir Magashi, ya bayyana hakan ne yayin zantawar shi da manema labarai a zauren majalisar wakilan tarayya ranar Talata yayinda ake tantance sabbin hafsoshin tsaron da shugaba Buhari ya nada. Ministan ya ce hafsoshin tsaron za su bazama aiki ana kammala tantancesu. Yace: “Mun nuna bajintarmu wajen dakile irin wannan matsalan.…

Read More

Buhari Ya Yi Tir Da Sace ?aliban Jihar Neja

Shugaban ?asa Muhammadu Buhari yayi Allah-wadai da sace dalibai da ma’aikatan makarantar GSSS dake Kagara, jihar Neja a ranar Talata da wasu ‘yan Bindiga suka yi. Mai magana da yawun shugaban kasa Femi Adesina ne ya wallafa jawaban shugaban kasan a shafinsa na Facebook a ranar Laraba da yammaci. A cewar shugaban, ya samu labarin faruwar lamarin kai harin ‘yan ta’adda da ya auku cikin dare, wanda har ya zuwa yanzu ba a gano adadin ma’aikata da daliban da aka sace ba. Shugaban ya kuma kara da cewa ya tura…

Read More

Neja: Ba Zan Biya Ku?in Fansar ?aliban Da Aka Sace Ba – Gwamna

Gwamna Abubakar Sani-Bello na jihar Neja ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta biya kudin fansa ga masu satar yaran makarantar Kwalejin Kimiyya ta Gwamnati da ke Kangara ba, karamar hukumar Rafi ta jihar. Bello ya bayyana hakan ne lokacin da yake zantawa da manema labarai a ranar Laraba, bayan sace wasu dalibai da ma’aikatan Kwalejin a daren Talata. Idan ba a manta ba jaridar muryar ‘yanci ta kawo maku ruhoton yadda wasu yan ta’adda suka sace dalibai a makarantar kwana na gwamnati dake kagara.ko karshen shekarar data gabata anyi…

Read More

Da ?umi-?umi: An Yi Garkuwa Da ?alibai Da Malamai A Jihar Neja

A daren ranar Talata ne da misalin karfe 2 na dare, wasu ‘yan bindiga suka shiga makarantar kwana ta Kagara dake jihar Neja, inda suka garkuwa da wasu dalibai da malaman makarantar. Wani mazaunin rukunin gidajen malaman makarantar, ya shaida wa Aminiya yadda ‘yan bindigar suka tattara daliban da malaman, sannan suka yi awon gaba da su. An gano yadda ‘yan bindigar sanye da kayan sojoji suka sulale da wanda suka sace din, ba tare da samun agaji daga jami’an tsaron jihar ba. Ya zuwa yanzu kakakin ‘yan sandan jihar,…

Read More

Shi’a Ta Wallafa Littafin Arangamarsu Da Soji A Zariya

Kungiyar yan Shi’a ta Islamic Movement in Nigeria (IMN), ta bukaci a yi wa mambobinta sama da dubu daya da ta yi zargin an hallaka a 2015 adalci. Kungiyar ta sake neman wannan bukata ce a wurin bikin kaddamar da wani littafi na musamman da ‘yan Shi’a din suka wallafa a kan abubuwan da suka faru a rikicin sojojin Nijeriya da mambobin mazhabarsu a Zaria jihar Kaduna shekaru shida da suka wuce. Jaridar Daily Trust ta ce Farfesa Isa Hassan Mshalgaru da ya yi bitar littafin mai suna ‘December 2015…

Read More

Rungumar Zaman Lafiya Ne Mafita Ga ‘Yan Najeriya – Tsohon Shugaban Kasa

Tsohon Shugaban kasa kuma shugaban kwamitin zaman lafiya na kasa, Janar Abdulsalami Abubakar mai ritaya ya nemi a rungumi zaman lafiya kan abubuwan da suka faru kwanan nan na hare-haren kabilanci a fadin kasar. Hakazalika ya bukaci sabbin shugabannin tsaro da Sufeto-Janar na ‘yan sanda a kan su tashi tsaye a wannan lokacin don shirya kyawawan dabarun kawo karshen mummunan abubuwan da ke faruwa a kasar. Abdulsalami wanda ya nuna rashin jin dadinsa game da rikice-rikicen da ke faruwa a kasar, ya koka kan cewa idan ba a kula da…

Read More

Za Mu Hukunta Duk Bafillacen Da Aka Samu Da Aikata Laifi – Buhari

Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya nesanta kansa daga aika-aikar wasu Fulani a cikin Najeriya. Kamar yadda muka samu labari daga majiyar mu cewa Shugaba Buhari ya ce ba ya goyon bayan garkuwa da mutane da hallaka jama’a tare da barnar da wasu Fulani ke yi a cikin Nijeriya. A daidai lokacin da shugaba Buhari ke wannan jawabin, ya umarci Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya Karkashin Shugaban `Yan Sandan IGP Adamu Muhammad Abubakar da ya bayyana Sunayen Fulanin da ake shari’a da su a kotu Akan Zargin Su Da Aikata laifin garkuwa…

Read More

Ba Bahaushe Ne Ya Tayar Da Rikicin Shasha Ba – Shaidar Gani Da Ido

Wata shaidar gani da ido ta bada labarin abinda ya faru a kasuwar Shasha da ke Ibadan a jihar Oyo da ya yi sanadin mutuwar a kalla mutane 20 da asarar dukiyoyin miliyoyin naira. A bidiyon da ya bazu a ranar Litinin, wata shaidar gani da ido da ta ce sunanta Nana Aisha ta yi gyara game da ikirarin da aka yi da farko na cewa wani bahaushe ne ya kashe bayarabe inda ta ce wani dan Nijar ne, mai sana’ar tura baro. Ta ce rikicin da ya faru tsakanin…

Read More

Domin Kare Kai Na Bu?aci Makiyaya Su Rin?a Yawo Da Manyan Makamai

Gwamnatin jihar Bauchi ?ar?ashin jagorancin Gwamnan Jihar ?auran Bauchi ta kara haske a kan jawabin Gwamna Bala Mohammed inda yace makiyaya su dinga yawo da Manyan Bindigogi ?irar AK-47 domin ba kansu kariya. A wata takarda da aka fitar a ranar Lahadi 14 ga watan Fabrairu, Mukhtar Gidado wanda babban mai ba gwamnan shawara ne a kafafen sada zumunta ya ce ba a fahimci tsokacin ubangidansa bane, ko ka?an maganarshi ba tana nufin tayar da hankali ban sai dai kawai neman mafita ta kare kai ga Fulani. Idan za a…

Read More

Makamai Jami’an Tsaro Ke Bu?ata Ba Addu’a Ba – El Rufa’i

Mai girma Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir Ahmad El-Rufa’i, ya ce hukumomin tsaron Nijeriya suna bukatar makamai na zamani ba addu’a ba kafin su iya magance ta’addanci da ‘yan ta’adda dake addabar kasar musamman yankin Arewacin Kasar. El-Rufa’i ya bayyana hakan ne yayin taro na musamman da aka gudanar tsakanin gwamnonin jihohin arewa maso yamma da Malaman addinai gami da sarakunan gargajiya a Kaduna Cibiyar Arewa. Mai ba Shugaban kasa shawara a kan harkokin tsaro, Babagana Monguno, ne ya jagoranci tawagar wakilan gwamnatin tarayya a wurin taron wanda aka shirya…

Read More

An Tura ‘Yan Sandan Kwantar Tarzoma Jihar Oyo

Shugaban ‘yan Sandan Najeriya Mohammed Adamu, ya ba da umarnin tura rundunoni hudu na ‘yan sandan kwantar da tarzoma don magance rikice-rikicen da ke faruwa a wasu sassan jihar Oyo domin shawo kan Matsalar. Rundunonin ‘yan Sandan masu shiga tsakanin sun ha?a da rundunar kwantar da tarzomar ?ar?ashin Ofishin Jami’an leken Asirin na kasa da kuma sashin jirage masu saukar ungulu dake kula da sa-ido daga sashen jigilar ‘yan sanda. Jihar ta Oyo ta kasance cikin rikici a kwanan nan, ciki har da kashe-kashen da ake zargin makiyaya da yi…

Read More

Matsalar Tsaro: A Daina ?ora Laifi Akan Gwamnatin Tarayya Ka?ai – Ministan Tsaro

Gwamnatin tarayya ta bukaci gwamnonin Jihohi da sauran wakilai da su ba da tasu gudummawar wajen magance ‘yan Bindiga da sauran matsalolin tsaro da ke addabar al’ummar kasar, ba wai ?ora laifi akan Gwamnatin Tarayya ka?ai ba. Ministan Tsaro, Manjo Janar Bashir Salihi Magashi mai ritaya ya yi wannan furucin a ranar Asabar a Kano bayan ya sake jaddada rajistarsa na jam’iyyar APC a shiyyarsa ta Galadanchi da ke ?aramar hukumar Gwale ta Jihar Kano. Da yake amsa tambaya kan matsayar da gwamnatin tarayya ke da ita a kan ‘yan…

Read More

Majalisa Ta Sanya Ranar Tantance Sabbin Shugabannin Tsaro

Shugaban kwamitin sa ido kan harkokin rundunar soji a majalisar Dattawa, Sanata Ali Ndume ya ce kwamitin ha?aka na majalisar Dattawa kan harkokin tsaro da suka hada da na rundunar tsaro, sojin kasa, sojin ruwa da sojin sama za su fara tantance sabbin hafsoshin tsaron Nijeriya a cikin makon da zamu shiga. Ndume ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ke amsa tambayoyi daga manema labarai Abuja. A ranar Larabar da ta gabata ne shugaban majalisar dattijan Ahmad Lawan, ya mika bukatar shugaban kasa Muhammadu Buhari na amince da…

Read More

Miyyeti Allah Ta Yi Kiran A Bada Dama ‘Yan Najeriya Su Mallaki Bindigogi

Kungiyar Miyetti Allah Cattle Breeder’s Association of Nigeria (MACBAN) ta shawarci Gwamnatin Tarayya da ta kyale kowane dan Najeriya ya mallaki bindigogi don kare kansa duba da kalubalen tsaro dake addabar kasar. Kungiyar ta yi wannan kiran ne yayin da take mayar da martani a kan kalaman da Gwamnan Bauchi, Sanata Bala Mohammed, ya yi cewa makiyaya suna dauke da bindigogi ne kawai don kare kansu. Gwamna Mohammed ya sha suka sosai bayan goyon bayan makiyaya na yin amfani da AK-47 don kare kansu daga barayin shanu. Shugaban kungiyar ta…

Read More