Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Sabon Ministan Makamashi, Injiniya Abubakar Aliyu, ya ce Shugaba Muhammadu Buhari ya tura shi ya karbi ragamar shugabanci a ma’aikatar ne saboda wani dalili na musamman na cancanta.
An ruwaito cewa Aliyu ya bayyana hakan ne yayin da ya kama aiki a Ma’aikatar Makamashi a Abuja a ranar Litinin.
Da ya ke yi wa direktoci da ma’aikatan ma’aikatar jawabi, ya ce: “Na san kun yi aiki sosai, Na zo nan ne domin in taimaka muku, ko da ba ku ko babu ku domin abin da aka turo ni in tabbatar shine mu yi nasara. Wanda ya dauke ni aiki ya turo ni nan ne saboda wani dalili.”
Da ya ke bayyana dalilin, Sabon Ministan Makamashin ya ce an turo shi ne domin ya tabbatar an yi komai yadda ya dace a bangaren makamashi. Aliyu ya kuma nemi hadin kan masu ruwa da tsaki yana cewa; “Ba hanayenku kadai na ke so ba wurin aiki har da zuciyarku, nan ne gaskiya da jajircewa ya ke.
“Aikin mu zai taba rayukan dukkan yan Nigeria don haka na zo nan ne domin in kara wa aikin ku inganci.”
