Buhari Zai Kaddamar Da Sabbin Samfurin Takardun Naira A Yau

Shugaban ?asa Najeriya Muhammadu Buhari zai ?addamar da sabbin takardun ku?in naira da aka sake wa fasali ranar yau Laraba.

Gwamnan babban bankin ?asar CBN Godwin Emefiele ne ya bayyana haka ga manema labarai ranar Talata a wajen taron kwamitin tsare-tsaren ku?i.

Mista Emefele ya ce babban bankin ?asar ba zai sauya ranar ?arshe da ya saka na mayar da tsoffin ku?in zuwa bankunan ?asar domin sauya su da sabbin takardun ku?in ba.

Ya ?ara da cewa shugaban zai ?addamar da sabbin takardun ku?in a lokacin taron majalisar zartarwa na ?asa.

Tun da a ranar 26 ga watan Oktoba ne dai gwamnan babban bankin ?asar ya sanar da cewa za a sauya fasalin wasu takardun ku?in ?asar, inda ya ce sabbin ku?in za su fara yawo daga ranar 15 ga watan Disamba, inda za a ci gaba da kashe su tare da tsoffin ku?in har zuwa ranar 31 ga watan Janairun 2023, lokacin da za a daina karbar tsoffin ?udin.

Related posts

Leave a Comment