Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya yi tir da Allah wadai da kisan uku daga cikin ?aliban da aka sace a Jami’ar Greenfield a Jihar Kaduna.
“Tunanina yana tare da iyalansu a wannan lokacin na jimami. Allah Ya ji?ansu, ”in ji Shugaban cikin sanarwar da Malam Garba Shehu ya fitar a ranar Asabar.
Shugaban ya la’anci yawaitar kashe –kashe da sace-sacen mutane a Kaduna, wanda ya kira “munanan hare-haren ta’addanci.”
Shugaban ya kuma bayyana takaici yana mai cewa “abin ba?in ciki ne yadda wasu shugabannin siyasa da na addini ke ?ara rura wuta da ?ara zafin ?unci ga iyalan mamatan da ke zaman makoki.”
“Wannan bala’in na bu?atar nuna tausayi da kuma ha?in kai a matsayinmu na al’umma don tunkarar wa?annan ?alubale da kuma barazana ga dimokura?iyyarmu da zaman lafiyar kasa,” in ji shugaban.
Shugaban ya ce ” Najeriya za ta yi amfani da duk ?arfinta domin ya?ar ?an fashi da masu satar mutane da kuma siyasar kashe-kashe.”
