Shugaba Muhammadu Buhari ya yi watsi da wasu karin ayyuka 6,576 da Majalisar Dokokin ?asar ta ?ara a kasafin kudin 2022.
Shugaban ya ce sanya ayyukan da ku?insu ya haura Naira biliyan 36 ya sa?a wa dokar cin gashin kai da kowanne ?angaren zartarwa ke da shi.
Shugaban wanda ya bayyana hakan yayin sanya wa kasafin hannu a fadarsa da ke Abuja, ya ce zai sake mayar wa ?an majalisar don su duba gyare-gyaren da ya yi.
Sai dai shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan ya kafe a kan cewa babu kuskure a abun da suka yi, yana cewa dama ba lallai ne a ce a ko da yaushe ra’ayin ?angarorin biyu ya zo ?aya ba.
