2023: Osinbajo Da Zulum Ya Kamata A Tsayar Takara – Jigon APC

Sanata Abubaka Girei, wani babban jigo a jam’iyyar APC mai mulki ya bayar da shawarar a ba Mataimakin Shugaban ?asa Farfesa Yemi Osinbajo da Gwamnan Jihar Borno Farfesa Babagana Zulum tikitin takarar Shugabancin kasa a 2023 domin kai wa ga samun nasara.

Sanata Abubakar Girbi ya ?ara da cewa yin wannan ha?in zai tabbatar da nasarar jam’iyyar APC mai mulki kuma zai zamanto wani babban alheri ga ‘yan Najeriya gaba daya.

Babban dan siyasar daga Jihar Adamawa kuma tsohon Sanata ya ce idan APC za ta mika shugabancin kasarta zuwa kudu, zai fi dacewa ta baiwa mataimakin shugaban kasa mai ci tikitin domin karfafa nasarorin Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Sanata Girei ya kara da cewa zabar gwamnan jihar Borno a matsayin abokin takarar Osinbajo zai taimakawa jam’iyyar wajen ci gaba da kasancewa a mulki har bayan 2023.

Tsohon Sanatan ya shawarci Shugabannin APC da cewar su yi karatun ta natsu su kauce wa yin gagarumin kuskure a zabinta na Shugaban kasa da abokin takararsa a kakar za?e ta 2023.

Duk da cewar ana kan fafutukar ganin an mika shugabanci ga kudu maso gabas, jigon na APC ya korafin cewa tunani mai kyau shine mika shi ga kudu maso yamma saboda goyon bayan da yankin ya baiwa Buhari a zaben shekarar 2015 da 2019.

Hakazalika, jigon na APC ya ce yanki mafi cancanta wajen samar da shugaban kasa a 2023 ita ce arewa maso gabas sai kudu maso gabas domin basu taba samar da Shugaban kasa a baya ba.

Related posts

Leave a Comment