Buhari Ya Na?a Sabon Shugaban Dakarun Soji

Rahotanni daga babban birnin tarayya Abuja na bayyana cewar mai girma Shugaban ?asa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Manjo Janar Yahaya Faruq a matsayin sabon Shugaban Dakarun Sojin Najeriya.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata takardar sanarwa da mai magana da yawun rundunar sojin Birgidiya Janar Onyema Nwacukwu ya fitar a yau Alhamis.

Kafin na?in nashi Manjo Janar Yahaya shine babban Kwamandan rundunar soji dake ya?i da ‘yan ta’adda a yankin Arewa maso gabashin Najeriya mai suna Operation Ha?in Kai.

Nadin nashi na zuwa ne ‘yan kwanaki ka?an da rasuwar tsohon shugaban Dakarun Sojin Janar Ibrahim Attahiru da wasu Soji goma a wani mummunan hatsarin jirgin sama da ya afku a jihar Kaduna.

Ana sa ran sabon Shugaban Dakarun Sojin wanda ya fito daga Jihar Sokoto ?aramar Hukumar Bo?inga zai cigaba daga inda marigayi Janar Attahiru ya tsaya a ya?i da matsalar tsaro da ta addabi Najeriya musamman yankin Arewacin kasar.

Related posts

Leave a Comment