Rahotanni daga Maiduguri babban birnin jihar Borno na bayyana cewar Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar ya fara azuminsa na watar Ramadana a mahaifarsa, karamar hukumar Mafa dake tsakiyar jihar ta Borno.
Zulum a jawabin da ya fitar ranar Asabar, 2 ga watan Afrilu, ya bayyana cewa da kansa ya jagoranci rabawa talakawa buhuhunan kayan abinci saboda shigowar watan na azumi.
A cewar jawabin, akalla mutum 15,327 aka rabawa kudi a hannu da buhunanan shinkafa da sukari, da kuma atamfa na dinkin Sallah.
“Wadanda suka amfana sun hada da mata 9,313 da Maza 6,014; kowanne cikinsu ya samu N5000 inda aka raba jimillan N76,635,000:00.”
“Bayan kudin, kowane magidanci ya samu buhun shinkafa 50kg da Shadda yadi biyar; yayin da kowace mace ta samu turmin atamfa da sukari 10kg.”
