Shugaba Buhari Muhammadu na Nijeriya har wayau a wannan shekarar ta 2021 shi ne shugaban da ya fi sauran takwarorinsa na Nahiyar Afrika talauci.
Kamar yadda mujallar Forbes da Washington suka bayyana, cikin shekaru sama da shida da shugaban ya kwashe yana mulkar Nijeriya adadin ku?a?en da ya mallaka a lalitarsa shi ne Dala 150,000 wato kwatankwacin naira miliyan 30 , sannan sai gidaje 5 da kuma wa?ansu gidaje biyu na ?asa, ?aya a mahaifarsa dake Daura sannan ?aya a Katsina. Sai kuma garken shanu guda 270, tumakai 25 , dawakai 5 da kuma gonar noma.
Ha?i?a duk da kasancewa shugaban yana da wa?ansu kura-kurai a mulkinsa, amma ya sha bamban da shugabannin ?asar na baya wa?anda suka wawure dukiyar ?asar suka arzurta kawunansu da ?a?ansu.
Daga Mutawakkil Gambo Doko
