Rahotanni daga Maiduguri babban birnin Jihar Borno na nuna cewa Mayakan Boko Haram sun hallaka wasu dakarun soji har guda shidda a wani harin kwantan ?auna da suka kai musu a yankin Baga.
Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya auku ne a jiya Asabar a daidai kauyen Kwayamti dake kan hanyar zuwa Baga. Sannan kuma bincike ya nuna cewa har da wani dan bangan sa kai shi ma ya rasa ransa.
Idan ba a manta ba dai, a jiya Asabar din ne Gwamna Zulum da tawagar sa suka sake kai ziyara garin Baga, bayan harin da ‘yan Boko Haram suka kaiwa tawagarsa a yayin wata ziyara da ya kai garin Bagan dake jihar Borno a kwanakin baya.
Sha’anin tsaro na ?ara shiga cikin mawuyacin hali a jihar Borno da ke yankin Arewa maso gabashin Najeriya, inda maya?an Ta’adda na Boko Haram da takwararsu na ISWAP ke addabar yankin da yawan hare hare.
Gwamnan Jihar Borno Babagana Zulum ya bayyana a kwanakin baya cewar rayuwarshi tana cikin hatsari, sakamakon halin da Jihar ke shiga a kusan kullum da fargabar kai mishi hari da ‘yan ta’addan ke ?o?arin yi a kusan kullum.
