Kaduna: ?ungiyar Ansaru Ta Haramta Siyasa

?ungiyar Ansaru dake ikirarin kishin addinin Musulunci ta haramta duk wasu al’amura da ke da ala?a da siyasa a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna.

Kungiyar ci gaban Masarautar yankin ta ce yanzu haka kungiyar ta shimfida wasu sharu??a da suka dace da salon shugabancinta, kuma duk wanda aka samu da sa?a su, yana iya fuskantar hukunci mai tsanani.

Bayanan da BBC ta tatattara sun bayyana cewa kungiyar ta raba wa jama’a wani sa?o da ke ?unshe da dukkan manufofinta, ciki har da na kawo ?arshe dimukradiyya da harkokin siyasa a yankin.

A yanzu dai mutanen garuruwan da dokar ta shafa, kan saci jiki zuwa wasu wuraren ne don gudanar da tarukan siyasa sa’ad da duk bukatar hakan ta taso.

Related posts

Leave a Comment