Wakilin ?asar Amurka, Ambasada Green, ya ce tsarin za?en shugaban ?asa da INEC ta shirya babu gaskiya a cikin sa ko mis?ala zarra.
Green ya fa?i haka ne a lokacin da yake zantawa da tashar talabijin ta Arise Tv a Babban Birnin Tarayya Abuja.
Ya kuma ?ara da cewa INEC ta kunyata Najeriya da nahiyar Afrika baki daya. Sahihancin sakamakon su ba abin dogaro ba ne sam, Inji shi.
Ina mai nuna ba?in ciki na tare da duk yawan biliyoyin kasafin kudin wannan zabe da a ka kashe amma babu wani sakamako mai inganci da har za a iya yin alfahari da shi, a cewar sa.
