Hukumar kula da mutane masu bu?ata ta musamman ta Nijeriya NCPD, ta ce ta tallafa wa kimanin tsaffin sojoji 700 wa?anda aka sallama daga aiki saboda sun samu nakasa a lokacin da suke ya?i da Boko Haram.
Babban Sakataren hukumar James Lalu ya bayyana haka a lokacin da ya bayyana gaban kwamitin Majalisar Dattawa kan ayyuka na musamman domin kare kasafin ma’aikatarsa na ba?i.
Lalu wanda ya ce akwai nakasassu a Nijeriya da yawansu ya kai miliyan 31.5 kuma adadin na da?a ?aruwa, ya bu?aci a ?ara yawan ku?in da ake ware wa hukumar don su yi daidai da bu?atar ayyyukanta.
Ku kasance damu a shafin mu na www.muryaryanci.com domin samun ingantattun ruhotanni da dumi dumin su
