Binuwai: Dakarun Soji Sun Yi Wa ‘Yan Bindiga Kisan Kiyashi

Rahoton dake shigo mana daga Jihar Binuwai na bayyana cewar dakarun Soji sun yi nasarar harbe ‘yan bindiga da dama wadanda ke barna a karamar hukumar Kastina-Ala da sauran kananan hukumomi a jihar.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Shugaban karamar hukumar Kastina-Ala, Alfred Atera, ya shaida cewa, shugaban ‘yan bindigan, Terna Gide, ya yi barazanar kai hari kauyukan da ke kusa da shi, inda aka kashe mutanensa masu yawa.

“Bayan harin da dakarun Sojin suka kai a sansanin Tse-Keji a ranar Talata inda aka karkashe ‘yan bindigan, an lalata musu sansaninsu tare da tattara muggan makamai da tarin wasu layu.

“A ranar Talata sojojin da ke Gbise da ke Kastina-Ala sun gudanar da rangadin share fage har sai da suka ci karo da ‘yan bindiga a Tse-Keji, an yi musayar wuta amma sojojin sun ci karfinsu. “Saboda haka, ‘yan bindigar da ke dauke da makamai sun gudu cikin daji cikin rudewa amma sojoji sun fatattake su, kuma an kashe ‘yan bindigan da dama”.

Related posts

Leave a Comment