Bauchi: Gwamna Bala Ya Yi Tir Da Yanke Al’aurar ‘Yar Shekara 6

Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed na Jihar Bauchi yayi Allah wadai da tofin alatsine game da yanke gaban wata yarinya mai shekaru shida da haihuwa a garin Jama’re akan neman duniya, tare da bada tallafin kudi naira Miliyan N1m don yi mata magani da samun lafiya.

Gwamnan wanda kwamishinan kananan hukumomi, da na kiwon lafiya, da ta mata da kuma kakain Gwamnan Jihar Mukhtar Gidado suka wakilceshi a ziyarar jajanta ma iyayen yarinyar da abun ya faru da ita a karamar hukumar Jama’are.

Yayin da yake jawabin sakon gwamnan kwamishinan kananan hukumomi Abdurrazak Nuhu Zaki, yace gwamna Bala bai jidadin abunda ya faru ba, yace shiyasa ya turo su domin suyi jaje a madadin gwamnatin Jihar, tare da bada gudimuwar miliyan daya domin fara yi mata magani.

Kana yace Gwamnan yasha alwashin aiwatar da hukunci kan wanda ya aikata hakan, yace wan nan rashin Imani ne da rashin tsoron Allah da kuma ganganci, yace zai dandana kudarsa matuka gaya.

Tun a farko dai wani yaro ne dan shekara ashirin da haihuwa ake zargin ya aikata wan nan mummunan aiki akan yarinyar, inda tuni hukumar Yan”sanadan Jihar ta tabbatar da aukuwan wan nan al’amari inda tace mai laifin yana hannumta, kuma tana ci gaba da bincike kan wan nan batu.

Tawagar gwamnatin Jihar tana isa Asibitin Malam Amimu kano dake birnin na kano, sun iske yarinyar kwance shame- shame akan gadon asibiti tana karbar magani

Kwamishinan ya kara da cewa a lokacin da suke ganawa da iyayen, wan nan abu ya munana kuma gwamnati baza tasa idanu ba kawai, ana cin zarafin mata ko ta wanni fani, kana yace hukunci mai tsanani zaifuskanta saboda ya zama ishara ga yan baya.

Sa anan yace “a cikin tallafin harda kayan abinci da aka mika ma iyayen wan nan yarinya, da kuma yin alkawarin daukan dukkan dawainiyar samun lafiyar ta daga aljihun gwamnatin Jihar”

Bugu da kari itama Uwargidan Gwamnan Jihar, Aisha Bala tace tuni ta shirya lauyoyi da zasu tsaya ma yarinyar a Babban kutu don tabbatar da hukunci mai tsanani akan wanda ya aikata hakan, inji kwamishiyar mata Hajara Gidado.

Daga karshe iyayen yarinyar da akayi mata wan nan aika aika sunyi godiya ma Gwamnan Jihar Bala Mohammed da yinkurinsa na ganin yarsu ta samu gata domin fitar da ita daga wan nan kangi da aka jefa ta a ciki

Har ila yau likitan dake duba lafiyarta Dr. Kawu Magashi, yace za ayi mata aiki irin na (Plastic Surgery) domin dawo mata da martabarta, nan take suka mika kudin tallafin na naira miliyan guda ga hukumarasibitin da kuma iyayen.

Daga Adamu Shehu Bauchi

Related posts

Leave a Comment