Jigawa: An Ba Karuwai Wa’adin Wata Guda Su Fitar Da Mazan Aure

Rahotanni daga Karamar hukumar Gwaram ta jihar Jigawa na bayyana cewar ?aramar Hukumar ta dauki sabbin matakai a yakin da ta ke yi da mata masu zaman kansu inda ta basu wa’adin kwanaki 30 su fice daga yankin ko kuma a aurar da su.

Matan masu zaman kansu wadanda ba yan asalin jihar ko karamar hukumar bane za a mayar da su garuruwansu na asali muddin wa’adin ya cika ba su gabatar da Mazan Aure ba.

Rahoton ya kuma ce wadanda kuma yan gari ne da ke da niyyar tuba su sauya sana’arsu su tabbata sun shirya yin aure. An umurci su mika sunanayensu da na mazan da za su aure su kafin wa’adin da aka basu na kwanaki 30 ta cika.

Shugaban karamar hukumar Gwaram, Zaharadden Abubakar ya ce: “karamar hukumar a shirye ta ke ta dauki nauyin aurar da mata masu zaman kansu yan asalin karamar hukumar idan sun shirya su bar sana’ar.”

A wani taro da aka yi a garin Sara, wata fitacciyar kasuwar da ke ci mako-mako a karamar hukumar, Abubakar ya umurci dukkan mata masu zaman kansu da ke yankin su mika wa karamar hukuma sunayen mazan da ke harka da su kafin karshen wa’adin.

Ya kuma bada umurnin rufe dukkan gidajen casu da gidajen shan giya a karamar hukumar nan take ba tare da bata lokaci ba.

Related posts

Leave a Comment