Rahotanni daga Jihar Bauchi na bayyana cewar Gwamnatin jihar ta sanyawa sabon sansanin alhazan jihar sunan me alfarma Sarkin Musulmi Sultan Sa’ad Abubakar.
Da yake jawabi yayin bude sansanin, mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar ya fara da yabawa Gwamna Bala Muhammad kan samar da sansanin da a cewar sa ya dace da zamani.
Wannan na kunshe cikin jawabin da hadimin gwamnan Bauchi na kafafen yada labaran zamani, Lawal Muazu Bauchi ya saki.
Sultan Sa’ad yace sanya sunan sa ga sansanin babban kalubale ne akan sa na tabbatar da anyi amfani da kula da shi yadda ya kamata. Sarkin Musulmi Sa’ad yayi kira ga Gwamna Bala Muhammad da kada yayi kasa a guiwa wajen cigaba da samar da ayyukan raya jihar Bauchi.
A nasa tsokacin, Gwamna Bala Muhammad yace sansanin ya kunshi ofisoshin jami’an hukumar kula da jin dadin alhazai, asibiti, masallaci, kasuwar zamani da wuraren kwanan maniyata.
Yace gina sansanin ya biyo bayan kalubale da wahalhalu da maniyyata ke fuskanta a tsohon sansanin na wucin-gadi dake Games Village inda ya kara da cewa gwamnatinsa zata tabbatar da an kula tare da aiki da shi ta hanyoyin da suka dace.
