Babu Wani Katabus Da Gwamnatin Buhari Ta Yi A Yaki Da Rashawa – Muhammad Saleh

An bayyana cewar babu wani katabus ko wani abin azo gani da gwamnatin Buhari ta aiwatar a fannin ya?i da rashawa a tsawon shekaru da Buhari ya lashe a karagar mulki.

Bayanin hakan ya fito ne daga bakin wani mai nazarin al’amuran siyasar Najeriya mai suna Alhaji Muhammad Saleh a yayin wata tattaunawa da gidan Talabijin na Liberty ya yi dashi kai tsaye cikin shirin “Ina Dalili”.

Muhammad Saleh ya cigaba da cewar hakika ‘Yan Najeriya sun gaji da gafara Sa basu ga kaho ba tsawon lokaci a ?a?atun da gwamnatin Buhari ke yi na ya?i da cin Hanci da rashawa.

Ya bayyana Kujerar shugaban hukumar EFCC a matsayin kujera mai zafi wanda zama kanta sai wanda ya shirya duba da yadda a tarihin wadanda suka ri?e shugabancin hukumar ba su sauka ta da?in rai ba, wanda hakan ya biyo yadda manya suka sanya wa kujerar ido.

Muhammad Saleh ya shawarci shugaban hukumar Abdulrasheed Bawa da tsayuwar daka gami da tabbatar da mallakar hujja kafin tuhuma.

Ya kuma kalubalanci Ministan Shari’a na ?asa Abubakar Malami da cewar nauyi ne wanda ya rataya a wuyan shi ya tabbatar duk wanda hukumar ta gurfanar a kotu an yanke mishi hukunci cikin gaggawa ba tare da bata lokaci ba.

Related posts

Leave a Comment