Neman Mafita: Za A Tsaurara Haraji Akan ‘Yan Najeriya – Ministar Kudi

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar duk da halin ?a?a-ni-ka-yin da ‘yan Najeriya ke ciki na ?uncin rayuka da rashin tsaro, Ministar Harkokin Ku?a?e Zainab Ahmed ta bayyana cewa akwai yiwuwar gwamnatin tarayya ta fito da sabbin hanyoyin kar?ar haraji cikin shekarar 2022, mai kamawa nan da bayan makonni biyu.

Zainab ta ce akwai bu?atar ?arin samun ku?a?en haraji domin ?ara wa da?e makuba, tunda a cewar ta, “yanzu tattalin arzikin Najeriya ya hau mi?a??ar hanya da babu karkata ko waskiya.”

Zainab ta fitar da wannan furuci a lokacin da ta ke wa masu ruwa da tsaki jawabi wurin sauraren Kudirin Dokar Ku?a?e ta 2021, taron da Kwamitin Majalisar Tarayya kan Harkokin Ku?a?e ya shirya a ranar Litinin, a Abuja.

Ta ce a cikin ?udirin an gabatar da shawarwarin gyare-gyare, inda ta ce kuma wasu harajin ma za a ?ara fito da su a cikin tsakiyar shekarar 2022 ?in.

“Mu na nan mu na shirin bijiro da sabbin ?udirori a tsakiyar 2022.” Inji Zainab.

Sai dai kuma ta ce Ma’aikatar Harkokin Ku?a?e ta kauda kai daga yin magana kan Harajin ‘VAT’ da na ‘La’ada Waje’, saboda batutuwan su na kotu, saboda wasu sun shigar da gwamnatin tarayya ?ara a kan harajin biyu.

Idan ba a manta ba, Jihar Ribas ta yi nasara a Kotun Tarayya cewa ita ke da alhakin kar?ar harajin VAT ba tarayya ba, lamarin da Gwamnatin Tarayya ta ?aukaka ?ara.

“Tuni mun tsara ?udiri da daftarin yi wa dokokin ku?a?e kwaskwarima domin ?ara dan?ara haraji a ?asar nan. Musamman a ?angaren harajin cikin gida, tsarin tasarifin ku?a?en harajin, sai kuma harajin da ake kar?a daga kayayyakin da ake shigowa da su daga waje, sai harajin gyaran tsarin kar?ar harajin da kuma tsarin yadda gwamnati ke sarrafa ku?a?en harajin.

“Akwai daftarin gyaran Dokar Masu Manyan Hannayen Jari, Dokar Harajin Ku?a?en Shigar Kamfanoni, Dokar Kafa Hukumar Tara Haraji ta Tarayya (FIRS), Dokar Harajin Ku?a?en Shigar ?ai?aikun Mutane, Dokar Harajin La’ada Waje, Dokar Harajin Jiki Magayi da sauran su.

Related posts

Leave a Comment