Babban kwamandan ‘yan bindiga a jihar Zamfara mai suna Auwalu Daudawa ya ce ya amince ya mika bindigoginsa ne bayan ya gano kai hare-hare babu riba kuma babu amfani ko na sisi a ciki.
Auwalu Daudawa na daya daga cikin wadanda ke jagorantar yan bindiga da ke dajin Dumburum a karamar hukumar Zurmi a jihar Zamfara, Jihar ta yi suna wajen ta?ar?arewar tsaro a Najeriya.
Daudawa ya sanar da hakan ne a ranar Talata a hedkwatar ‘yan sanda da ke jihar Zamfara a Gusau, babban birnin jihar.
Ya ce ya yi imanin cewa wasu ‘yan bindigan a dazukan Zamfara suma za su bi sahunsa su mika wuya domin dama suna neman irin wannan damar.
“Yan banga da ake fi sani da ‘yan sakai suna matsa mana. “Hakan ne yasa muka dauki makamai amma duk da hakan ba su daina matsa mana ba. “Idan yan sakai (yan banga) suka cigaba da kashe fulani a kasuwanni da wasu wurare ba tare da shari’a ba ina baka tabbacin ba za a taba samun zaman lafiya ba.
“Amma mun goda wa Allah saboda shiryar da mu kan hanya madaidaiciya,” in ji shi.
