Al-Mundahana: Za A Gurfanar Da Tsohuwar Ministar Jiragen Sama

Hukumar ya?i da al-mundahana ta ?asa EFCC ta gurfanar da Stella Oduah, tsohuwar ministan sufurin jiragen sama gaban kuliya bisa zargin wawurar kudaden al’umma gami da rub da ciki ba bisa ?a’ida ba.

An ?age zaman da za a yi da ita a kotu ranar Talata saboda tsohuwar ministan bata nan, ko Lauyanta. Yanzu haka Uduah sanata ce mai wakiltar mazabar Anambra ta arewa, kuma ana zargin ta da wasu mutane 8 a wata kara mai lamba: FHC/ABJ/CR/316/20.

Hukumar tana zargin Oduah da kwasar kudin gwamnati lokacin tana minista. A ranar Talata lauyan EFCC, Hassan Liman, ya sanar da kotu cewa tsohuwar ministan bata riga ta shirya zuwa kotun ba, don haka ya bukaci alkali ya dage karar.

Kamar yadda yace, “Mai girma mai shari’a, yau ne aka gabatar da karar kuma na sanar da hukumar amma ba a riga an sanar da wacce ake kara (Oduah) ba. “Sakamakon haka ne muke bukatar a dan daga shari’ar.”

Iyang Ekwo, alkali mai shari’a yace aikin masu kara ne su gabatar da wanda suke kara gaban kotu. Don haka ya dage karar zuwa 22 ga watan Fabrairu.

Related posts

Leave a Comment