Rahotannin dake shigo mana daga Abuja na bayyana cewar Shugaban ‘yan sanda Usman Al?ali ya mayar da martani ga rahotannin da wasu kafafen yada labarai ke cewa jami’an ‘yan sanda na shirin zanga-zanga a ranar 26 ga Maris domin neman karin albashi da alawus.
Shugaban ‘yan sandan ya bayyana cewa babu dan sandan da zai kaskantar da kansa zuwa ga yin zanga-zanga kan karin albashi saboda suna sane da illar hakan.
A cikin wata sanarwa dauke da sa hannun mukaddashin kakakin rundunar, Muyiwa Adejobi, ya yi watsi da rahoton, yana mai cewa: “Kokarin wasu marasa kishin kasa ne na bata sunan rundunar, da batar da al’umma da kuma zafafa harkokin siyasa.”
“Tun daga lokacin da aka amince da hakan, hukumar albashi ta fitar da sanarwar aiwatar da hakan, mai girma ministan harkokin ‘yan sanda da kuma IGP suna nan suna ta aiki tare da hukumar FIRS domin tabbatar da dakatar da cire haraji kamar yadda Shugaban kasa da majalisar zartarwa ta tarayya suka yi umurni.”
A cewarsa, rundunar yan sanda hukuma ce mai tsari da da’a tare da shiryayyun sharudda da ka’idoji don magance koke-koke kuma babu yajin aiki a cikin tsarin.
