Babu Gaskiya A Labarin Mun Koma PDP – Yari Da Marafa

Rahotanni daga Jihar Zamfara na bayyana cewar tsohon gwamnan jihar Abdul’aziz Yari, da tsohon sanata daga jihar, Sanata Kabiru Marafa sun musanta rahoton cewa sun koma PDP.

A ranar Asabar ne mutane suka yi ta ya?a labarin a kafafen sada zumunta cewa mutanen biyu sun fice daga APC kuma sun koma PDP.

Jita-Jitar ta bayyana cewa jiga-jigan APC biyu sun gana da tsohon shugaban majalisar dattijai, Sanata Bukola Saraki, a wani biki a Kaduna.

Kakakin tsohon gwamna Yari, Ibrahim Muhammad, kuma tsohon kwamishinan ya?a labarai na jihar Zamfara, yace wannan ?agaggen labari ne kawai.

Ya kuma kara da cewa makiyan tsohon gwamnan Zamfara a siyasa ne suka kirkiri labarin domin cimma wata manufa ta su.

A nasa ?angaren, da yake musanta rahoton a wata sanarwa da ya fitar, Kabir Marafa, ya kira jitar-jitar da, “Tunanin wasu tsiraru dake bakin cikin cigaba da ganin su a APC.”

“Kundin ?asar nan ya bamu damar ganawa, halarta, tattaunawa da kuma zuwa duk inda muke so tare da wanda muke so. Da gaske ne mun je Kaduna ?aura auren diyar Sheikh Bala Lau, shin hakan laifi ne?”

“Lokacin da tsohon mataimakin shugaban ?asa, Atiku Abubakar ya halarci ?aura auren ?an shugaban kasa Buhari, shin hakan ya nuna zai koma APC?”

“Da mu aka gina APC har ta zo matakin da take a yanzun, saboda haka ba zai yuwu wani ya ya?a jita-jitar da zata sa mu saki aikin da muka fara ga wasu mutane ba.”

Related posts

Leave a Comment