Babu Dan Bindigar Da Zai Saura A 2023 – Buhari

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban ?asa, Muhammadu Buhari, ya tabbatarwa yan Najeriya cewa gwamnatinsa zata kawo ?arshen ayyukan yan bindiga da ?alubalen tsaro kafin wa’adinsa ya ?are a 2023.

Buhari ya yi wannan furucin ne a fadar mai martaba Sarkin Musulmi dake Sokoto ranar Alhamis, yayin da ya kai masa ziyara, domin jajanta kisan da ‘yan Bindiga suka yi wa jama’a a jihar.

Shugaban ?asan ya nuna tsantsar damuwarsa game da halin da mutane ke ciki a arewa maso yamma, inda ya ce baya iya runtsawa ya yi bacci.

“Abun damuwa ne matu?a, al’umma ?aya da al’ada iri ?aya amma suna kashe junan su ba tare da wani kwakkwaran dalili ba.” Shugaban ?asa ya kuma tabbatar da cewa zai mi?a mulkin Najeriya bayan ya murkushe duk wata damuwa ta rashin tsaro da fa?uwar tattalin arziki.

Related posts

Leave a Comment