Babu Cigaban Da Za A Samu A Najeriya Nan Da Shekaru 4 Sai Bashi – Bankin Duniya

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Bankin Bayar da Lamuni na Duniya, IMF ya yi garga?i ga Gwamnatin Najeriya cewa idan ba ta tashi tsaye ba, to babu makawa nan da shekarar 2026 ku?a?en haraji da sauran ku?a?en shiga zai ri?a tafiya wajen biyan basussukan da gwamnatin ?asar ta ciyo ne.

Wakilin IMF a Najeriya Ari Aisen ne ya bayyana haka a cikin wani rahoton da ya fitar ranar Litinin a Abuja.

Bayanin dai ya na ?unshe ne a cikin Rohoton Halin da Tattalin Arzikin ?asashen Afrika ta Yamma ke ciki, wanda ya nuna tattalin arzikin Najeriya ya shiga garari matu?ar gaske.

Ya ce a halin yanzu kusan kashi 89 na ku?a?en shigar Najeriya na tafiya wajen biyan basussuka ne.

“Sannan kuma duk wata Najeriya na kashe naira biliyan 500 wajen biyan ku?a?en tallafin mai. Wannan ma ba hanya ba ce mai kai kowace ?asa tudun-mun-tsira.”

Related posts

Leave a Comment