Bayan da wasu jiga-jigan ‘yan siyasa suka gaza kai bantensu a neman takarar shugaban ?asa musamman a jam’iyyar PDP yanzu haka sun koma neman wasu kujerun da ba su kai waccan daraja ba.
Cikin irin wa?annan ‘yan siyasa akwai gwamnan jihar Bauchi, wanda a yanzu ya koma neman takarar kujerar da yake kai, bayan wanda ya samu takarar gwamman jihar ya janye aniyarsa.
A jihar Sokoto ma da akwai irin wannan magana, inda gwamnan jihar da ya nemi takarar shugaban kasa zai koma neman kujerar sanata.
